Operation FANSAN YAMMA: Sojoji sun dakile yunƙurin sace fararen hula da dama a Zamfara
Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA , sun dakile wani yunƙurin garkuwa da fararen hula da ’yan ta’adda suka yi a ƙauyen Unguwar Rogo da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara. A yayin farmakin, sojojin sun kuɓutar da fararen hula tara , ciki har da wani jariri. A cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar haɗin gwiwar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 16 ga Agustan 2026 , lokacin da wasu ’yan ta’adda, waɗanda ake zargin wani jagoransu mai suna Mallam Shuaibu ne, suka kai hari kan fararen hula da ke
