AMMASCO RADIO NEWSROOM

top stories

An Yi Jana’izar Mijin Shugabar Tanzania

An yi jana’izar Hafidh Ameir Hassan, mijin Shugabar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, a Kizimkazi da ke Zanzibar. Marigayin, wanda aka haifa a ranar 1 ga Janairu, 1946, ya rasu ne a ranar Litinin, 7 ga Satumba, bayan fama da matsalar zuciya. Mataimakin Shugaban Tanzania, Deogratius Ndejembi, ne ya sanar da rasuwar, inda ya ce Hafidh Ameir Hassan ya rasu da misalin ƙarfe 8:00 na safe agogon ƙasar. Ya rasu ne a Asibitin Emilio Mzena Memorial da ke Zanzibar, inda yake karɓar magani. Jana’izar marigayin ta gudana a garinsu na Kizimkazi, inda iyalai, ’yan uwa da sauran al’umma suka halarta domin yi ma

Birtaniya Ta Ce Isra’ila Na Aikata Kisan Kiyashi a Yammacin Kogin Jordan

Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Ed Miliband, ya ce gwamnatin ƙasar ta amince da cewa Isra’ila na aikata abin da ta kira kisan kiyashi a wasu sassan Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye. Da yake jawabi a Majalisar Dokokin Birtaniya, Miliband ya zargi gwamnatin Isra’ila da yin biris da abubuwan da ke faruwa a yankunan Falasɗinawa. Ya ce Birtaniya ta daɗe tana kallon matsugunan Isra’ila da ke Yammacin Kogin Jordan a matsayin waɗanda suka saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa. Miliband ya kuma sanar da cewa gwamnatin Birtaniya ta ɗauki matsayar cewa mamayar da Isra’ila ke yi wa Yammacin Kogin Jordan ba t

Birtaniya Za Ta Hana Shigo da Kayayyakin Matsugunan Yahudawa

Gwamnatin Birtaniya na shirin hana shigo da kayayyakin da aka samar a matsugunan Yahudawa da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, ciki har da kayayyakin amfanin gona. Matakin na cikin wasu sauye-sauyen da gwamnatin Birtaniya ke shirin yi kan manufofinta game da Isra’ila, yayin da take ƙara matsa lamba kan ƙasar dangane da faɗaɗa matsugunan Yahudawa a yankunan Falasɗinawa da aka mamaye. A makon da ya gabata, Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Ed Miliband, ya shaida wa ’yan majalisar dokokin ƙasar cewa gwamnati na duba yiwuwar sauya wasu daga cikin tsare-tsaren da ke tsakaninta da Isra’ila. Gwamnato

An Kama Mutane 16 Kan Rikicin Ƙaramar Hukumar Dass.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta ce ta kama mutum kusan 16 da ake zargi da hannu a wani rikici da ya yi sanadin mutuwar mutane biyu a Ƙaramar Hukumar Dass. Rundunar ta ce ana binciken waɗanda aka kama kan zargin haɗa baki wajen aikata laifi, tayar da tarzoma da kuma kisan kai. Kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya shaida wa BBC cewa binciken farko ya nuna cewa lamarin ya fara ne a ranar 4 ga Satumban 2026, da misalin ƙarfe 6:00 na yamma. Ya ce wani mutum mai suna Ibrahim El-Safwan, wanda aka fi sani da Jabala’i, ya haɗa baki da wasu mutane tare da kai wa wani mai tuka babur mai kafa uku, Ab

Iyalin El-Rufai Sun Bai Wa Ministan Tsaro Wa’adin Kwanaki Bakwai

Iyalin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun bai wa Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, wa’adin kwanaki bakwai da ya janye wasu zarge-zargen da ya yi wa tsohon gwamnan ko kuma su ɗauki matakin shari’a a kansa. A wata sanarwa da ɗan tsohon gwamnan, Bello El-Rufai, ya fitar a madadin iyalan a ranar Litinin, ya ce Janar Musa ya yi zarge-zargen ne yayin wata hira kai tsaye da shirin Politics Today na Channels Television a ranar 3 ga Satumba. Sanarwar ta ce ministan ya zargi El-Rufai da shirya kashe mutane a Kudancin Kaduna a lokacin da yake gwamnan jihar. Sai da

Merz Ya Ce Jamus Na Fuskantar Sauyi a Siyasar Jam’iyyu

Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya ce ƙasar na fuskantar wani gagarumin sauyi a tsarin siyasar jam’iyyu, bayan da jam’iyyar AfD ta masu tsattsauran ra’ayi ta samu gagarumar nasara a zaɓen jihar Saxony-Anhalt da ke gabashin ƙasar. Merz ya ce sakamakon zaɓen ya zama babban abin damuwa ga jam’iyyar CDU mai ra’ayin mazan jiya, yana mai cewa akwai buƙatar jam’iyyar ta gudanar da nazari mai zurfi kan dalilan da suka haifar da wannan sakamako. Da yake magana kamar yadda jaridar Bild ta ruwaito, Merz ya ce akwai buƙatar jam’iyyar ta ƙara kusantar jama’a tare da ƙara ƙoƙari wajen fahimtar mat

Iran Ta Yi Barazanar Mayar Da Martani Kan Sabon Ƙudurin IAEA

Iran ta yi gargaɗin cewa za ta ɗauki matakan mayar da martani idan kwamitin gudanarwa na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya, IAEA, ya amince da sabon daftarin ƙudurin da ƙasashen Turai suka gabatar kan shirin nukiliyarta. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce ƙudurin na iya sake kai batun shirin nukiliyar Iran gaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya. Baghaei ya zargi ƙasashen Turai da komawa ga batun shirin nukiliyar Iran a duk lokacin da suka kasa cimma wasu daga cikin manufofinsu, yana mai cewa hakan wata hanya ce ta ƙara matsin lamba kan Tehran. Y

Mijin Shugabar Tanzania Ya Rasu

Mijin shugabar ƙasar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, Hafidh Ameir Hassan, ya rasu a yau Litinin, 7 ga watan Satumban 2026. Mataimakin shugaban ƙasar Tanzania, Deogratius Ndejembi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau. Sanarwar ta ce Hafidh Ameir Hassan ya rasu ne yayin da yake karɓar magani a Asibitin Emilio Mzena Memorial da ke Zanzibar, sakamakon wata matsalar lafiya da ta shafi zuciya. An ce ya rasu ne da misalin ƙarfe 8:00 na safe. Sanarwar ta ƙara da cewa tuni aka fara shirye-shiryen jana’izarsa, wadda za a gudanar a yankin Kizimkazi da ke Zanzibar.

Direbobi da ke bin titin Onitsha zuwa Owerri a Jihar Anambra sun koka kan yadda jami’an Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ke muzanta musu

Masu ababen hawa da ke bin titin Onitsha zuwa Owerri a Jihar Anambra sun koka kan yadda jami’an Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Anambra ke ci gaba da muzanta musu tare da kakaba musu tarar da suka ce ba ta dace ba, musamman a wuraren da titin ya lalace kusa da tashar People’s Club. Wasu daga cikin direbobin da suka zanta da jaridar Punch sun zargi jami’an hukumar da amfani da lalacewar titin wajen karbar kudade daga hannun masu ababen hawa. Sun ce ana karbar kudade tsakanin dubu N150 zuwa dubu N300 daga masu motoci na kashin kansu da direbobin tasi da na motocin haya da ke b

NUT reshen Karamar Hukumar Rogo a nan Kano ta ƙaddamar da shirin koyar da malamai 400 aikin sanyawa da gyaran na’urorin lantarki na Solar

Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Ƙasa NUT reshen Karamar Hukumar Rogo a nan Kano ta ƙaddamar da shirin koyar da malamai 400 aikin sanyawa, kulawa da gyaran na’urorin lantarki na Solar. Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Yaɗa Labarai na Karamar Hukumar Rogo, Abdu Bako Abdullahi, ya fitar. Sanarwar ta bayyana cewa, Shugaban NUT na Karamar Hukumar Rogo, Malam Aliyu Suleiman, ya ce shirin zai bai wa malaman ƙarin ƙwarewar sana’a da za ta taimaka musu wajen samun abin dogaro da kai. Malam Aliyu Suleiman ya ce malamai 400 za su amfana da shirin, inda za a koya musu yadda ake sanya na’urorin Solar, kul

Amurka ta amince da sayar wa Saudiyya makamai na dala biliyan 5

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da amincewa da yarjejeniyar sayar wa Saudiyya makamai da kayan aikin soji da darajarsu ta kai dala biliyan biyar . A cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce Saudiyya ta nemi sayen dubban bama-bamai , da na’urorin jagorantar makamai masu linzami masu dogon zango. Ta ce yarjejeniyar ta kuma ƙunshi manyan makamai da kayayyakin gyara, sinadarai, da kuma ayyukan tallafin fasaha, dabarun sufuri da samar da kayayyakin da suka shafi makaman. A cewar Amurka, yarjejeniyar na daga cikin matakan ƙarfafa tsaron Saudiyya, wadda take ɗaya daga cikin ƙawayenta masu muhim

Nijar ta zargi Faransa da hannu a yunƙurin hargitsa ƙasar

Gwamnatin Nijar ta zargi Faransa a hukumance da goyon bayan wani yunƙurin hargitsa ƙasar da ta ce ya faru a ranakun 28 da 29 ga watan Agusta . A cikin wata sanarwa, gwamnatin ta ce arangamar da ta faru a sansanin sojin sama na 101 da ke Yamai tana da alaƙa da ƙasashen waje. Ta ce tana da “ƙwararan shaidu masu yawa” da suka shafi harin, kuma tana nazarin yiwuwar shigar da ƙara a gaban kotunan ƙasa da ƙasa. Gwamnatin Nijar ta kuma zargi Shugaban Faransa, Emmanuel Macron , da jagorantar wata ƙungiya ta mutane da hukumomi da ke goyon bayan yunƙurin, tare da zargin cewa wasu ƙasashen Afirka da ba t

Putin ya bayar da umarnin dakatar da hare-hare kan Kyiv na kwanaki uku

Fadar gwamnatin Rasha, Kremlin, ta ce Shugaba Vladimir Putin ya bayar da umarnin dakatar da hare-haren da ake kai wa Kyiv na tsawon kwanaki uku, a daidai lokacin da wakilan Shugaban Amurka Donald Trump ke shirin ziyartar Ukraine domin tattauna hanyoyin kawo ƙarshen yaƙin. Wakilan na Amurka, Steve Witkoff da Jared Kushner , sun isa Moscow, inda ake sa ran za su gana da Shugaba Putin kafin su zarce zuwa Kyiv domin ganawa da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky. Wannan ne karon farko da Witkoff da Kushner za su kai irin wannan ziyara a Ukraine. Shugaba Trump ya ce wakilan na ɗauke da wata sabuwar

Arangama a Yemen ta kashe sama da mutane 60

Akalla mutane 60 ne suka mutu sakamakon sabuwar arangama tsakanin dakarun gwamnatin Yemen da ke samun goyon bayan Saudiyya da mayaƙan Houthi, kamar yadda majiyoyin lafiya da na soji suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP. Rahoton ya ce an shafe sa’o’i ana gwabza faɗa a wani yanki da ke kudu maso yammacin Yemen, inda aka kashe sojojin gwamnati 26 . A gefe guda kuma, majiyoyin lafiya da na soji na ƙungiyar Houthi, wadda Iran ke goyon baya, sun ce mayaƙansu 31 ne aka kashe a arangamar. Har ila yau, fararen hula na cikin waɗanda suka mutu, bayan da wani hari da makami mai linzami ya afka

Koriya ta Kudu na shirin tura sojoji zuwa mashigin Hormuz

Kafofin yaɗa labarai na Koriya ta Kudu sun ruwaito cewa gwamnatin ƙasar na shirin tura sojoji da kayan aiki domin tallafawa abin da ta kira “’yancin zirga-zirga a mashigin Hormuz” , tare da fara aikin kafin ƙarshen wannan shekara. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito a ranar Alhamis, 3 ga Satumba, cewa majiyoyin gwamnati da na soja sun ce Seoul na ɗaukar matakan doka domin samun amincewar majalisar dokoki kan tura sojojin. Rahotannin sun ce an riga an tattauna shirin a wani taron majalisar ministoci, yayin da ake shirin gabatar da buƙatar amincewa a hukumance ga majalisar dokokin ƙ

An ceto ma’aikata biyu da ransu bayan sama da mako guda a cikin rami a Nepal

An ceto wasu ma’aikata biyu da ransu daga tashar samar da wutar lantarki ta ruwa ta Trishuli 3A a Nepal, sama da mako guda bayan wata mummunar ambaliyar ruwa ta kwatsam ta afku a yankin tsaunukan Himalaya. An bayyana ma’aikatan da aka ceto da sunayen Sanjaya Shah da Kabir Maharjan , inda hukumomi suka ce an kwashe su ta jirgin sama zuwa wani asibiti a birnin Kathmandu domin samun kulawar lafiya. Dukkansu sun samu raunuka a hannaye da ƙafafuwa, wadanda hukumomi suka ce mai yiwuwa sun samu ne sakamakon yadda suka shafe kwanaki suna rarrafe a cikin wani rami da ke karkashin kasa. Masu aikin ceto

Mutane 37 sun mutu sakamakon shaƙar hayaƙin mai a Ribas

Aƙalla mutum 37 ne aka ruwaito sun mutu bayan sun shaƙi hayaƙi mai guba yayin da ake zargin wasu mutane da satar man fetur a wani wurin sauke kaya na jiragen ruwa a Jihar Ribas. Lamarin ya faru ne a daren Alhamis a Okari Jetty , da ke yankin Okrika, inda ake zargin wasu matasa daga Okrika da ƙauyukan da ke makwabtaka da yankin sun taru domin kwashe man fetur daga wani wurin da aka yi wa bututun mai ƙulli ba bisa ƙa'ida ba. Rahotanni sun ce fiye da mutum 100 ne suka isa wurin da ƙananan kwale-kwale, yayin da wani jirgin ruwa ke loda man fetur a yankin. An ce matsalar ta fara ne bayan wani ƙamsh

Gwamnan Plateau Ya Jagoranci Taron Majalisar Tsaro Kan Halin Tsaron Jihar

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya jagoranci taron Majalisar Tsaro ta Jihar a ranar Laraba, domin duba halin tsaro a jihar, yayin da rundunar ’yan sanda ta tabbatar da kama wasu da ake zargi da hannu a hare-haren baya-bayan nan. An gudanar da taron ne a Sabon Gidan Gwamnati da ke Little Rayfield, Jos, a daidai lokacin da wasu al’ummomin jihar ke fuskantar hare-hare. Tattaunawar ta mayar da hankali kan sabbin barazanar tsaro, hare-haren da suka faru kwanan nan, tattarawa da musayar bayanan sirri, matakan kariya, haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, da hanyoyin kare rayuka da dukiyoyi ta

Netanyahu Ya Ce Gwamnatin Iran Za Ta Ruguje Nan Ba Da Jimawa Ba

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce yana da yaƙinin cewa gwamnatin Iran za ta ruguje nan ba da jimawa ba. Netanyahu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wani taro da manyan jami’an sojin Isra’ila suka halarta, inda ya ce gwamnatin Iran na cikin wani yanayi na rauni fiye da kowane lokaci. “Yanzu gwamnatin Iran na cikin wani yanayi mai matuƙar rauni. Ta fi kowane lokaci a baya rauni, kuma tana ƙoƙarin tabbatar da kanta ne kawai,” in ji shi. Firaministan Isra’ilan ya ƙara da cewa yana da yaƙinin cewa za a iya kawar da abin da ya kira barazanar Iran gaba ɗaya, tare da kawo ƙarsh

Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani Ya Rasu Bayan Shekara 46 A Kan Sarauta

Sarkin Gumel da ke Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Muhammad Sani, ya rasu bayan shafe shekara 46 yana kan karagar mulkin masarautar. Sakataren Masarautar Gumel, Alhaji Murtala Aliyu, ne ya tabbatar wa BBC rasuwar sarkin a yau Alhamis, a birnin Alƙahira na ƙasar Masar. A cewar sakataren masarautar, marigayin ya shafe kusan makonni shida yana jinya a wani asibiti da ke Alƙahira kafin rasuwarsa. Sarkin ya kasance ɗaya daga cikin sarakunan arewacin Najeriya da suka fi dadewa a kan karagar mulki. Sakataren masarautar ya ce marigayin shi ne sarki na 16 a jerin sarakunan Masarautar Gumel, kuma shi ne sark