AMMASCO RADIO NEWSROOM

top stories

Janar Christopher Musa Ya Gargaɗi Jami'an Tsaro Kan Jinkirin Ɗaukar Mataki A Kan 'Yan Ta'adda

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, ya gargaɗi jami'an tsaro da su guji jinkiri wajen ɗaukar mataki a kan 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane yayin gudanar da ayyukansu. Janar Musa ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba yayin rabon motocin sulke da sauran kayan aikin tsaro ga hukumomin tsaro a jihar Sakkwato, inda ya sake jaddada aniyar gwamnatin tarayya na ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro a faɗin ƙasar. Ya ce duk wani jami'in tsaro da aka tura bakin aiki bai kamata ya tsaya jiran wani ƙarin umarni ba idan ya fuskanci barazana daga 'yan ta'adda ko 'yan bindiga. A ce

Kotu Ta Tura Tsohon Shugaban Kotun Ɗa'ar Ma'aikata, Danladi Umar, Gidan Gyaran Hali

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Maitama, Abuja, ta ba da umarnin tsare tsohon shugaban Kotun Ɗa'ar Ma'aikata ta Najeriya (CCT), Danladi Umar, a gidan gyaran hali na Kuje. Mai shari'a Peter Kekemeke ne ya bayar da umarnin bayan Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume guda huɗu da suka shafi zargin cin zarafin ofis da kuma karɓar kuɗaɗe ba bisa ƙa'ida ba. EFCC ta yi zargin cewa Danladi Umar ya yi amfani da asusun bankin matarsa a shekarar 2021 wajen karɓar Naira miliyan 5.5 daga wani kamfani da ya samu kwangilar fentin hedi

Iran Ta Ce A Shirye Take Ta Kare Kanta Daga Duk Wani Hari Na Amurka

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya bayyana cewa ƙasarsa a shirye take ta kare kanta idan har Amurka ta ci gaba da kai mata hare-hare. A wata tattaunawa ta waya da ya yi da Babban Hafsan Sojojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, Araqchi ya bayyana kalaman wasu jami'an Amurka na baya-bayan nan a matsayin abin da ya ce na nuna yiwuwar karya yarjejeniyoyin da aka cimma da kuma ƙara rura wutar rikici. Ministan ya kuma yi Allah wadai da hare-haren da Amurka ta kai kan wasu yankuna a Iran, yana mai cewa hakan ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da kuma Kundin Tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya

EFCC Ta Gurfanar Da Bello Bodejo Kan Zargin Hada-Hadar Kuɗaɗe Ba Bisa Ƙa'ida Ba

Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta gurfanar da shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta ƙasa, Bello Bodejo, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin gudanar da mu'amalar kuɗaɗe da ta haura dala miliyan 2.63 ba tare da bin tanade-tanaden doka ba. An gurfanar da Bodejo a gaban Mai Shari'a Inyang Ekwo kan tuhume-tuhume guda 12 da EFCC ta gabatar. A cewar EFCC, ana zargin Bodejo da karɓar tsabar kuɗi dala 200,000 daga tsohon Akanta Janar na Jihar Bauchi, Sa'idu Abubakar, a ranar 21 ga Janairun 2022, lamarin da hukumar ta ce ya saɓa wa dokokin da

Sufeto Janar Na 'Yan Sanda Ya Yi Kira Da A Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Hukumomin Tsaro Na Duniya

Sufeto Janar na Rundunar 'Yan Sandan Najeriya (IGP), Olatunji Rilwan Disu, ya sake jaddada aniyar Najeriya na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin 'yan sanda na ƙasashe daban-daban domin bunƙasa zaman lafiya, tsaro da ci gaba mai ɗorewa a duniya. IGP Disu ya bayyana hakan ne yayin halartar Taron Koli na Biyar na Shugabannin Hukumomin 'Yan Sanda na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNCOPS 2026), wanda aka gudanar daga ranar 7 zuwa 8 ga Yulin 2026 a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke birnin New York na Amurka. Taron ya haɗa ministoci, sufetocin janar na 'yan sanda, shugabannin hukumomin tsaro da

Majalisar Dattawa Ta Binciki Kashe-Kuɗen Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma

Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Harkokin Raya Yankuna ya fara bincike kan yadda Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma (NWDC) ke gudanar da harkokinta da kashe kuɗaɗenta. 'Yan majalisar sun nuna damuwa kan yadda aka kashe kusan Naira biliyan 1.19, inda suka yi zargin cewa kimanin Naira miliyan 943, wanda ya kai kusan kashi 79 cikin ɗari na adadin, an kashe su ne wajen biyan alawus-alawus na mambobin hukumar. Kwamitin ya kuma tambayi dalilin da ya sa Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ita ce kaɗai daga cikin hukumomin raya yankuna da ba ta da daraktocin gudanarwa da kuma ma'aikata, duk d

Farashin Ɗanyen Mai Ya Tashi Bayan Rikicin Tsagaita Wuta Tsakanin Amurka Da Iran

Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya tashi da sama da kashi biyar cikin ɗari a ranar Laraba, bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Amurka da Iran ta rushe. Bayan wannan sanarwa, farashin ɗanyen mai na Brent, wanda ake amfani da shi a matsayin ma'aunin kasuwar mai ta duniya, ya haura zuwa dala 78.09 kan kowace ganga. Rahotanni sun nuna cewa masu zuba jari da masu sa ido kan kasuwannin duniya na ci gaba da bibiyar yadda rikicin ke ƙara ta'azzara, saboda tasirinsa ga samar da makamashi da kasuwannin duniya. Tun kafin wannan

Hare haren mayakan JNIM yayi sanadiyar mutuwar akalla sojojin Burkina faso 50 da Yan banga

Aƙalla sojojin Burkina Faso da kuma ƴan bangar VDP da ke taimaka musu 50 ne aka kasha, a wasu hare-hare da mayaƙan JNIM da ke da alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda suka kai, yankuna daban daban na ƙasar a ranar Asabar ɗin da ta gabata. Tuni ɗai ƙunigiyar JNIM ta ɗauki naukin kai harin, tare da wallafa wasu hotunan yadda lamarin ya faru a shafukan sada zumunta. A cewar wata majiya, mayaƙan masu iƙirarin jihadin sun kai harin farko ne a sansanin soji da ke lardin Sourou, da misalin ƙarfe 5 na asubahin Asabar da ta gaba, inda suka kashe sojoji 23 da ƴan bangar VDP 11. Bayaga wannan hari ƙungiyar ta kuma

Takaddama Ta Kaure Kan Rahoton IMF Game Da Kashe Kuɗaɗe Da Bashin Gwamnatin Najeriya

Takaddama ta ɓarke tsakanin gwamnatin Najeriya da jam’iyyun adawa bayan wani rahoto ya haifar da ce-ce-ku-ce kan yadda aka kashe wasu kuɗaɗe da kuma yadda gwamnati ke ci gaba da karɓar bashi. Jam’iyyun adawa sun yi zargin cewa akwai alamun rashin gaskiya wajen tafiyar da kuɗaɗen gwamnati, musamman yayin da ake tunkarar zaɓe. Sun danganta hakan da wani rahoto da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya fitar, wanda ya yi nuni da cewa wasu kashe-kuɗaɗe da suka kai kusan tiriliyan 8.8 naira ba su shiga cikin kasafin kuɗin gwamnati ba. Rahoton ya nuna cewa waɗannan kashe-kuɗaɗen sun kai kusan kashi biyu c

Nijeriya Za Ta Binciki Manyan Kamfanonin Fasaha Kan Amfani Da Labaran Kafofin Yaɗa Labarai

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Hukumar Kula da Gogayya da Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kayayyaki ta Nijeriya (FCCPC) da ta gudanar da bincike kan manyan kamfanonin fasaha, ciki har da Meta, Alphabet (Google), X da wasu kamfanonin da ke haɓaka fasahar kirkirarriyar basira (AI), bisa zargin amfani da dabarun hana gogayya da kuma anfani da labaran kafafen yaɗa labaran Nijeriya ba tare da bin ƙa'ida ba. A wata sanarwa da FCCPC ta fitar, ta ce matakin ya biyo bayan wata takardar ƙorafi da Ƙungiyar Kamfanonin Yaɗa Labarai ta Nijeriya (NPO) ta shigar. Ƙungiyar na wakiltar manyan kamfanonin

A ranar litinin za a yi addu’ar cika shekara da rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari

Tsohon mai taimaka wa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan harkokin yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya sanar da shirin gudanar da addu'o'i da taron tunawa da cika shekara ɗaya da rasuwar tsohon shugaban ƙasar. A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Bashir Ahmad ya ce za a gudanar da taron ne a ranar Litinin, 13 ga Yulin 2026, domin tunawa da rayuwa, gudunmawa da kuma hidimar da Buhari ya yi wa Najeriya. Ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai jajircewa, gaskiya, ɗa'a da kishin ƙasa, yana mai cewa irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Najeriya za ta ci gaba da kasancewa ciki

Tanzaniya Ta Tura Sojoji Da Ƴansanda Gabanin Zanga-zangar Ƙasa

Gwamnatin Tanzaniya ta tura dakarun soji da jami’an ‘yansanda zuwa manyan biranen ƙasar gabanin wata zanga-zangar ƙasa da aka shirya gudanarwa ranar Talata, domin neman sauye-sauyen dimokuraɗiyya da kuma adalci kan zaɓen shekarar 2025 da ake takaddama a kansa. Mahukunta sun dakatar da duk wasu tarukan siyasa tun daga ranar 26 ga Yuni, inda suka bayyana cewa matakin na da nufin tabbatar da tsaro. Sai dai ‘yan adawa sun yi Allah-wadai da wannan mataki, suna mai cewa yana tauye ‘yancin jama’a da kuma hana gudanar da harkokin siyasa cikin ‘yanci. Jami’an tsaro sun ce sun samu bayanan sirri da ke n

Matatar Dangote Ta Fitar da Man Jirgin Sama na Naira Biliyan 757 Zuwa Turai

Matatar Man Dangote ta ci gaba da faɗaɗa kasuwancinta a duniya, bayan da ta fitar da man jirgin sama da darajarsa ta kai kusan naira biliyan 757 zuwa ƙasashen Turai a cikin watan Yuni. Rahotanni sun nuna cewa jimillar man da aka fitar ta kai tan 466,000, wanda ya yi daidai da kusan lita miliyan 582.5, lamarin da ya zama mafi girman adadin man jirgin sama da Najeriya ta taɓa fitarwa zuwa Turai tun bayan da matatar ta fara samar da wannan nau'in mai a shekarar 2024. Bayanan sun kuma nuna cewa Najeriya ta zama ƙasa mafi girma wajen samar wa Turai man jirgin sama a watan Yuni, inda ta fitar da tan

Gwamnatin tarayya ta shawarci 'yan Najeriya da ke zaune a Afirka ta Kudu da su fice daga kasar idan rayuwarsu na cikin hatsari

Gwamnatin tarayya ta shawarci 'yan Najeriya da ke zaune a Afirka ta Kudu da ke jin rayuwarsu na cikin hadari su yi amfani da damar jiragen da gwamnati ta tanada domin komawa gida, inda jirgin ƙarshe zai isa ranar 10 ga Yuli, 2026. Ministar harkokin waje, Ambasada Bianca Odumegwu Ojukwu, ta bayyana hakan a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, tana mai cewa har yanzu babu alamun inganta tsaro sakamakon hare-haren ƙyamar baƙi da ake ci gaba da kai wa a ƙasar. Ta ce gwamnati ta nuna damuwa musamman bayan kashe wasu 'yan Najeriya biyu, Musa Yunana Joe da Charles Iroegbu, tare da buƙatar hukumom

Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyoyin Naira Ba Tare da Kasafin Kuɗi ba

Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da zargin cewa ta kashe sama da naira tiriliyan 8 ba tare da an tanadi kuɗin a cikin kasafin kuɗi ba, tana mai cewa an yi kuskuren fassara rahoton Asusun Lamuni na Duniya (IMF). Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa gwamnatin ba ta da wani "kasafin kuɗi na ɓoye", yana mai jaddada cewa duk wani kuɗin da ake kashewa yana gudana ne bisa amincewar Majalisar Dokoki da kuma tanadin doka. Ya ce wasu kashe-kashen gwamnati da suka haɗa da ayyukan raya ƙasa, biyan basussuka da kuma ayyukan gaggawa na tsaro, doka ta ba su damar gudana, don haka bai dace a bayyana su

NDLEA ta kama wata taohuwa yar Shekara 67 dake zaune a birtaniya dauke da kilo 13 na Hodar ibilis a Legas

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA ta kama wata tsohuwa 'yar Najeriya mai shekaru 67 da ke zama a Birtaniya, Misis Mary Barek, bisa zargin yunƙurin safarar kilogram 13 na hodar iblis da aka ɓoye cikin bawon ayaba na bogi ta Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Murtala Muhammed da ke Legas. Hukumar ta ce an kama wacce ake zargin, wadda ke aiki a matsayin mai kula da marasa lafiya a Birtaniya, a sashen masu fita na Terminal 2 na filin jirgin a ranar Lahadi, 28 ga Yuni, yayin da take ƙoƙarin hawa jirgin kamfanin Virgin Atlantic zuwa birnin Landan. A cikin wata sanarwa da D

Tinubu Ya Jaddada Aniyar Gwamnatinsa na Kare Ƴancin Addini a Najeriya

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare ƴancin gudanar da addini tare da ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabambantan addinai a faɗin ƙasar. Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Abuja yayin da ya karɓi baƙuncin Sakataren Hulɗa da Ƙasashe da Ƙungiyoyi na Vatican, Archbishop Paul R. Gallagher, wanda ya kai masa ziyara tare da rakiyar Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Bianca Ojukwu. Shugaban ya ce tattaunawa da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai na daga cikin muhimman hanyoyin da za su taimaka wajen magance mats

Rundunar Soji Ta Ce Ana Ci Gaba da Ƙoƙarin Ceto Ɗaliban da Aka Sace a Oyo

Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya tabbatar da cewa dakarun soji na ci gaba da gudanar da ayyukan ceto domin kuɓutar da ɗalibai 39 da malamai bakwai da aka yi garkuwa da su a Jihar Oyo. Janar Shaibu ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar a birnin Fatakwal, Jihar Rivers, a yayin bukukuwan Ranar Sojojin Najeriya ta shekarar 2026. An sace ɗaliban da malamansu ne a ranar 15 ga Mayu, 2026, daga makarantu uku da ke Ƙaramar Hukumar Orire a Jihar Oyo. Ya ce jami'an tsaro na ci gaba da aiki ba dare ba rana domin ganin an ceto waɗand

Tsohon Shugaban Rasha ya jagoranci tawagar ƙasar zuwa jana'izar Ayatollah

Mataimakin shugaban Majalisar Tsaron Rasha kuma tsohon shugaban ƙasar, Dmitry Medvedev , ya isa birnin Tehran domin jagorantar tawagar ƙasarsa a jana'izar tsohon Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei . A filin jirgin saman Imam Khomeini International Airport , Gwamnan Babban Bankin Iran, Nasser Hemmati , ne ya tarbe shi tare da sauran jami'an gwamnatin ƙasar. Ziyarar Medvedev na nuna irin kusancin dangantakar da ke tsakanin Rasha da Iran, musamman a wannan lokaci da Iran ke gudanar da zaman makoki da shirye-shiryen jana'izar marigayi Khamenei. Ana sa ran shugabanni da manyan jami'ai dag

Za Mu Sallami Duk Wanda Aka Kama da Takardun Bogi — Gwamna Radda

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda , ya sha alwashin sallamar duk wani ma'aikacin gwamnati da aka samu ya samu aiki ta hanyar amfani da takardun bogi. Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wani taro a jihar, inda ya ce ba za a lamunci cuwa-cuƙwar takardun neman aiki ba, musamman a ɓangaren ilimi, saboda hakan na da illa ga ci gaban jihar. "Wanda ya yi cuwa-cuƙwar takarda aka ɗauke shi aiki, ba shi da aiki... siyasa kuma idan ya ga dama ya je ya zaɓi Fir'auna," in ji Gwamna Radda. Ya ƙara da cewa: "In ba da ka da takarda aka kore ka aiki sai me? Ko gobe muka kama wanda ba shi da takarda, korar