AMMASCO RADIO NEWSROOM

top stories

Ofishin tsohon shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad ya karyata cewa Isra’ila ta masa tayin daukarsa aiki

Tsohon shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad a ranar Talata ya ƙaryata wani rahoto na The New York Times da ke zargin cewa hukumar leken asiri ta Isra'ila, Mossad, ta nemi ɗaukar shi aiki haka kuma an yi masa ɗaurin-talala, inda ya bayyana ikirarin a matsayin “ƙarya tsagwaronta.” A cikin wata sanarwa, ofishin Ahmadinejad ya zargi jaridar da wallafa rahotannin da aka ƙiƙira don yaudarar ra'ayin jama'a da ƙara haddasa rarrabuwar kai a cikin gida a Iran. Ofishin ya kuma ƙaryata cewa Ahmadinejad yana ƙarƙashin ɗaurin-talala, inda ya ce wannan ikirarin an ƙirƙire shi ne domin tallafa wa abin da suka kw

Gwamnatin Jihar Neja ta haramta wa makarantu masu zaman kansu gudanar da bukukuwan kammala karatu (Graduation Ceremony), tare da maye gurbinsu da Bukukuwan Jawabi da Raba

An ƙaddamar da wannan tsari ne ta hannun Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu ta Jihar Neja, da nufin daidaita shirye-shiryen ƙarshen zangon karatu da kuma magance abin da hukumomi suka bayyana a matsayin tatsar iyaye kudi da tsada da nuna isa a makarantu masu zaman kansu. A cikin wata sanarwa da Daraktan Sashen Ayyukan Yaɗa Labarai na Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta jihar, Yunusa Ibrahim , ya fitar, gwamnatin ta ce maimakon bukukuwan kammala karatu, makarantu su riƙa gudanar da Bukukuwan Jawabi da Raba Kyaututtuka domin karrama ɗalibai da suka yi fice a karatu, kyawawan ɗabi'

Jirgin karshe na yan najeriya mazauna kasar afrika ta kudu dauke da mutane 315 zata isa gida a gobe laraba 15 ga watan yuli,2026

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin Ma'aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Imomotimi Ebienfa , ya sanya wa hannu a ranar Talata. Sanarwar ta ce jirgin Air Peace ne zai gudanar da jigilar, inda zai tashi daga Afirka ta Kudu da ƙarfe 1:30 na safe , inda ake sa ran zai sauka a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Murtala Mohammed da ke Legas da misalin ƙarfe 6:30 na safe . Tun da farko dai Gwamnatin Tarayya ta gabatar da jirage huɗu na aikin kwaso 'yan Najeriya zuwa gida, inda ta dawo da ɗaruruwan mutane sakamakon hare-haren ƙiyayya ga baƙi (xenophobia) da kuma matsalolin tsaro da suka fa

Iran ta ce ta harbo jirgi mara matuƙi na Amurka a Bandar Abbas

Rundunar sojin Iran ta yi iƙirarin cewa dakarun tsaron sararin samaniyarta sun harbo wani jirgi mara matuƙi na Amurka a sararin samaniyar birnin Bandar Abbas da ke kudancin ƙasar. Kamfanin dillancin labarai na Mehr , wanda gwamnatin Iran ke da iko a kansa, ya rawaito cewa rundunar sojin ta ce an gano tare da lalata jirgin ne a yankin da ke tsakanin Bandar Abbas da Hajiabad , bayan tsarin tsaron sararin samaniyar ƙasar ya gano motsinsa. A cewar rundunar, an kakkaɓe jirgin ne yayin da dakarun tsaron sama ke mayar da martani ga abin da ta bayyana a matsayin hare-haren maƙiya da kuma ƙoƙarin kare

Kotun Sudan ta yanke wa jagoran RSF Hemedti hukuncin ɗaurin rai da rai

Wata kotu da ke Port Sudan ta yanke wa jagoran rundunar Rapid Support Forces (RSF) , Mohamed Hamdan Dagalo , wanda aka fi sani da Hemedti , hukuncin ɗaurin rai da rai. Kotun ta yanke hukuncin ne a shari'ar da aka gudanar ba tare da Hemedti ya halarta ba, inda ta same shi da laifukan kisan ƙare dangi, aikata laifukan yaƙi, laifukan cin zarafin bil'adama , da kuma kai hare-hare kan fararen hula. Hukuncin, wanda aka yanke ranar Lahadi, 12 ga Yulin 2026 , shi ne mafi tsauri da aka taɓa yanke wa jagoran RSF tun bayan ɓarkewar yaƙin Sudan a shekarar 2023 . Shari'ar ta fi mayar da hankali kan kisan t

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin jarrabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarrabawar WAEC da NECO ga ɗaliban makarantun sakandire, domin ba da damar sake nazarin matakin tare da ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki. A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya ta fitar, ta ce an ɗauki wannan mataki ne bayan shawarwari da ra'ayoyi da aka samu daga jama'a kan shirin. Tun da farko, ma'aikatar ta sanar da aniyar ƙara kuɗin rajistar jarrabawar daga naira 27,000 zuwa naira 50,000 , wanda aka shirya fara aiwatarwa daga shekarar 2027 . Ma'aikatar ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki da sauran matsalo

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa ta gano wasu 'yan ƙasashen waje uku da ke cikin mayaƙan ƙungiyar ISWAP

A cikin wata sanarwa da rundunar Operation Hadin Kai , mai yaƙi da Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabashin ƙasar ta fitar, ta ce an gano mutanen ne bayan da sojoji suka ƙwato wata kyamara a yayin wani artabu da mayaƙan ISWAP a yankin Cross Kauwa da ke Jihar Borno. Sanarwar ta ce hotuna da bayanan da ke cikin kyamarar sun taimaka wajen gano mutanen uku. Daga cikinsu akwai wani Bafalasɗine mai suna Abu Ishaq , wanda rundunar ta ce shi ne babban mai horas da mayaƙan ƙungiyar. Haka kuma, an gano wani mai suna Abu Thaiba , wanda aka bayyana a matsayin likitan ISWAP. Sai kuma wani mutum na uku, wa

Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin kara kudin jarrabawar WAEC da NECO ga daliban sakandire ta kasar

Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da shirin ƙara kuɗin jarabawar Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Makarantun Sakandare ta Yammacin Afirka (WAEC) da ta Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare ta Kasa (NECO), domin sake nazarin batun tare da tuntubar masu ruwa da tsaki. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta fitar, inda ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin bai wa gwamnati damar yin cikakken nazari kan shirin kafin yanke hukunci na ƙarshe. Tun da farko, ma’aikatar ta sanar da aniyar ƙara kuɗin jarabawar daga N27,000 zuwa N50,000 , wanda aka shirya zai

Wannan kamen ya biyo bayan wani kwantan ɓauna da maharan suka yi wa jami'an tsaro, amma dakarun suka fatattake su.

Hukumomin tsaron Jamhuriyar Nijar sun sanar da samun nasara a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin kasar, inda dakarun haɗin gwiwa suka yi nasarar cafke wasu ƴan bindiga 8 da suka kai hari. Wannan kamen ya biyo bayan wani kwantan ɓauna da maharan suka yi wa jami'an tsaro, amma dakarun suka fatattake su. Baya ga kama mutanen, jami'an tsaron sun yi nasarar kwace miyagun makamai masu tarin yawa, da sauran kayan yaki da ƴan ta'addan ke amfani da su wajen addabar al'ummar da ke makwabtaka da tafkin Chadi. An gudanar da wannan aiki ne a yankin kan iyaka da Najeriya, biyo bayan harin da aka kai wa o

Sanatan Amurka Lindsey Graham Ya Rasu Yana Da Shekaru 71

Sanata mai wakiltar jam'iyyar Republican daga jihar South Carolina a Majalisar Dattawan Amurka, Lindsey Graham, ya rasu yana da shekaru 71 bayan wata gajeriyar jinya. Ofishinsa ne ya sanar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar, inda ya bayyana alhinin rasuwar fitaccen ɗan siyasar. Lindsey Graham ya shafe sama da shekaru 20 yana wakiltar jihar South Carolina a Majalisar Dattawan Amurka, kuma ya kasance ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan jam'iyyar Republican. Haka kuma, an san shi a matsayin na kusa da tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump. Marigayin ya yi fice wajen bayyan

Tsohon Sarkin Qatar, Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani, Ya Rasu

Gwamnatin Qatar ta sanar da rasuwar tsohon Sarkin ƙasar, Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani, wanda ya rasu yana da shekaru 74 a duniya. Sheikh Hamad ya jagoranci Qatar daga shekarar 1995 zuwa 2013, kuma ana masa kallon ɗaya daga cikin shugabannin da suka taka muhimmiyar rawa wajen gina Qatar ta zamani da kuma ɗaga martabarta a idon duniya. A lokacin mulkinsa, ƙasar ta samu gagarumin ci gaban tattalin arziki, musamman ta fuskar albarkatun iskar gas da bunƙasar ababen more rayuwa, lamarin da ya mayar da Qatar ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi bunƙasa a yankin Gabas ta Tsakiya. Har ila yau, a sh

Wasu matasa a Maidugurin Jihar Borno, sun gudanar da zanga-zangar adawa da matsalar tsaro

Matasa da ɗalibai a Jihar Borno sun gudanar da zanga-zanga a ranar Lahadi domin nuna adawa da rashin tsaro, tare da kira ga ‘yan Najeriya da su mara wa gwamnati baya su kuma haɗa kai wajen yaƙi da ta’addanci da sauran nau’o’in laifuffuka a ƙasar. Gangamin wayar da kan jama’a mai taken #UniteAgainstTerror ya haɗa ƙungiyoyin ɗalibai da na matasa daga sassa daban-daban na jihar. An gudanar da tattakin wayar da kan jama’ar ne a yankin Post Office da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Da yake zantawa da Jaridar PUNCH Online kai tsaye a wurin zanga-zangar, shugaban Matasa da Ɗalibai na Jihar

Masar Da Qatar Sun Yi Kira Ga Amurka Da Iran Su Koma Kan Teburin Tattaunawa

Masar da Qatar sun yi kira ga Amurka da Iran da su dawo kan teburin tattaunawa domin neman mafita ta lumana ga rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu. Kiran ya fito ne daga Ministan Harkokin Wajen Masar, Badr Abdel Ati, da Firaministan Qatar kuma Ministan Harkokin Wajen ƙasar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, bayan wata tattaunawa ta wayar tarho da suka yi kan halin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki. A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Masar ta fitar, ministocin sun jaddada muhimmancin komawa kan hanyoyin diflomasiyya da sasanci, tare da buƙatar dukkan ɓangarorin su kauce

Hukumar Shari'a tace ba za ta amince da duk wani yunƙuri na buɗe masallatan Juma’a ba tare da bin ƙa’idojin da suka dace ba

Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta bayyana cewa ba za ta lamunci ci gaba da buɗe masallatan Juma’a ba tare da samun amincewarta ba. Kwamishina na Biyu a Hukumar, Sheikh Ali Danabba, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai. Sheikh Ali Danabba ya ce doka ta tanadi cewa duk wanda ke son buɗe masallacin Juma’a dole ne ya fara neman izini daga hukumar shari’a tare da cika sharuddan da aka gindaya. Ya jaddada cewa Hukumar ba za ta amince da duk wani yunƙuri na buɗe masallatan Juma’a ba tare da bin ƙa’idojin da suka dace ba, yana mai kira ga al’umma da su mutunta dokoki da tsare-tsar

Muhammad Ya Sake Zama Sunan Da Aka Fi Sanya Wa Jarirai A Ingila Da Wales

Sunan Muhammad ya sake zama sunan da iyaye suka fi sanya wa jariran maza a Ingila da Wales a shekarar 2025. Hukumar Ƙididdiga ta Birtaniya (Office for National Statistics) ce ta bayyana hakan a cikin rahoton shekara-shekara da ta fitar a ranar Alhamis kan sunayen da aka fi sanya wa jarirai a Ingila da Wales. Rahoton ya nuna cewa wannan shi ne karo na uku a jere da sunan Muhammad ke zama mafi shahara a tsakanin sunayen jariran maza, bayan ya jagoranci jerin sunayen a shekarun 2023, 2024 da kuma 2025. Sakamakon ya nuna ci gaba da karuwar shaharar sunan Muhammad a Ingila da Wales, inda ya ci gaba

Fubara Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.854 Na Shekarar 2026

Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya kai Naira tiriliyan 1.854 ga Majalisar Dokokin Jihar Rivers. Wannan shi ne karo na farko da gwamnan ya bayyana a gaban majalisar ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Martin Amaewhule, tun bayan rikicin siyasa da ya haddasa rabuwar kai a majalisar a shekarar 2023. Da yake gabatar da kasafin, Gwamna Fubara ya bayyana cewa an tsara shi ne domin ƙara bunƙasa tattalin arzikin jihar, inganta ayyukan more rayuwa, da kuma ƙarfafa zuba jari a sassa daban-daban. Kasafin kuɗin na shekarar 2026 ya nuna ƙarin kashi

Kotu a Kano ta fara sauraran karar zargin da ake yi wa Fatima Abdullahi na kashe saurayinta Isma'il sidi Buzu

Kotun majistret mai lamba 2 ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Auwal Yusuf Sulaiman, ta fara sauraron wata ƙara da gwamnatin jihar Kano, ta gurfanar da wata mata mai suna Fatima Abdullahi wadda aka fi sani da Sele mai kimanin shekaru 20. Ana zargin Fatima da laifin kashe saurayin ta mai suna Ismail Sidi wanda aka fi sani da Buzu. Binciken yansanda ya bayyana cewar, a waccan rana Fatima da marigayi Ismail sun yi rigima har kuma fatiman ta bubbagawa marigayin wani abu a kansa, inda jini yayi ta zuba. Har ila yau an kuma yi zargin cewar Fatima ta kunna wuta a gidan nata domin ta ɓatar da sawun binc

Amurka Ta Fitar Da Jerin Wasu 'Yan Najeriya Da Ake Shirin Kora Daga Ƙasar

Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka (DHS) ta wallafa jerin wasu 'yan Najeriya da take shirin kora daga ƙasar, a matsayin wani ɓangare na shirin gwamnatin Amurka na tsaurara matakan kan baƙin da ba su da takardun zama ko kuma waɗanda ake zargi ko aka samu da aikata laifuka. A cikin sanarwar da ma'aikatar ta fitar, ta bayyana cewa mutanen da ke cikin jerin na hannun Hukumar Kula da Shige da Fice da Kwastam ta Amurka (ICE), inda wasu daga cikinsu ke fuskantar zarge-zargen aikata laifuka daban-daban. Sai dai ma'aikatar ba ta bayyana ranar da za a fara aiwatar da korar mutanen ba. A cewar DHS, m

Sojojin Najeriya Sun Kama Wata Ƴar Chadi Bisa Zargin Kai Wa Boko Haram Miyagun Ƙwayoyi Da Giya

Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation Hadin Kai sun kama wata 'yar ƙasar Chadi da ake zargi da kai wa mayaƙan Boko Haram miyagun ƙwayoyi, giya da sauran haramtattun kayayyaki. A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar, ya ce an kama matar ne bayan wani aikin sintiri da ya samu nasara sakamakon ingantattun bayanan sirri. Ya ce a ranar 9 ga Yuli, dakarun sun cafke wadda ake zargin, Misis Rachael Samuel, mai shekara 48, 'yar garin Kelo da ke lardin Chari-Baguirmi na Jamhuriyar Chadi. Binciken farko, a cewar r

Wike: Yawancin Ayyukan Da Muka Kammala A Abuja Tsofaffin Ayyuka Ne Da Aka Yi Watsi Da Su

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa mafi yawan ayyukan da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kammala a Abuja tsoffin ayyuka ne da aka yi watsi da su tun gwamnatocin da suka gabata. Da yake ganawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Wike ya ce gwamnatin ta ba da fifiko wajen kammala ayyukan da ta gada kafin fara sabbin ayyuka. Ya bayyana cewa wasu daga cikin ayyukan sun shafe shekaru tsakanin 15 zuwa 16 ba a kammala su ba, amma gwamnatin Shugaba Tinubu ta ba da umarnin a farfaɗo da su domin kada a bar muhimman ayyukan gwamnati su lalace. A cewarsa, kusan kashi 60