Uwa ta nemi adalci kan zargin jami'in NDLEA da yi wa 'yarta mai shekara takwas fyaɗe
Mahaifiyar wata yarinya mai shekara takwas ta buƙaci a tabbatar da adalci bayan zargin cewa wani jami'in Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ya yi wa 'yarta fyaɗe a Jihar Bauchi. Lauyan mai shigar da ƙara, Barista Alƙasim Mohammed , wanda ke wakiltar ƙungiyar African Child Development and Human Right Protection , ya bayyana cewa mahaifiyar yarinyar na damuwa da jinkirin gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu. A cewar lauyan, lamarin ya faru ne lokacin da aka aika yarinyar sayo ruwan leda a gidan maƙwabcinsu, inda ake zargin wani jami'in NDLEA mai suna Muhammad Mus
