AMMASCO RADIO NEWSROOM

local

Sarkin Kano Sanusi II ya jagoranci Sallar Gani a karon farko

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II , ya jagoranci Sallar Gani a birnin Kano a karon farko, yayin da ɗaruruwan mahaya dawakai suka fito domin gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W). Sallar Gani wata tsohuwar al’ada ce da Masarautar Kano ke gudanarwa domin tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W), tare da nuna al’adun gargajiya da tarihin masarautar. A bana, an gudanar da hawan na tsawon kwanaki biyu, inda Sarkin Kano ya zagaya sassa daban-daban na birnin tare da rakiyar masu sarauta da mahaya dawakai, yayin da dubban mutane suka fito domin kallon bi

An sayar da kujerun aikin Hajjin 2027 gaba ɗaya a Kano

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da cewa an sayar da dukkan kujeru 3,050 da aka ware wa jihar domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2027 . Babban Daraktan Hukumar, Abubakar Ibrahim Matawalle , ya ce an samu nasarar ne bayan da hukumar ta buƙaci maniyyatan da ke buƙatar kujerun su gaggauta biyan kuɗaɗen Hajji tare da kammala dukkan takardun da ake buƙata. Ya bayyana cewa akwai sama da mutum 200 da ke jiran samun gurbi idan wasu daga cikin waɗanda suka samu kujeru suka gaza cika sharuddan tafiya. Matawalle ya kuma gargaɗi waɗanda suka biya kuɗin Hajji amma ba su gabatar da fasfo

Atiku Ya Soki Tafiyar Tinubu Zuwa Turai, Ya Ce Ƙasa Na Bukatar Shugabanci

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya soki tafiyar Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zuwa Turai, yana mai cewa shugaban ƙasar ya zaɓi yin hutu ne a lokacin da Najeriya ke fuskantar manyan ƙalubale. Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa, inda ya ce yanayin da ƙasar ke ciki na buƙatar shugaban ƙasa ya kasance tare da al’ummarsa domin fuskantar matsalolin da suke addabar su. Ya ce duk da cewa shi ma ya taɓa yin tafiye-tafiye tare da zama a ƙasashen waje, akwai babban bambanci tsakanin tafiyar mutum mai zaman kansa da kuma ta shugaban ƙasa mai ci.

Shugaba Tinubu zai bar Abuja a yau domin tafiya Turai don fara hutun makonni uku cikin hutunsa na shekara - shekara

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a yau domin tafiya Turai, inda zai fara hutun makonni uku a matsayin wani bangare na hutunsa na shekara-shekara. Birnin Landan na Birtaniya ne zai kasance zangonsa na farko a wannan tafiya. Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi. Sanarwar ta ce ana sa ran Tinubu zai dawo Nijeriya bayan kammala hutun, domin shiga cikin harkokin yakin neman zaben 2027.

Amurka Na Shirin Janye Sojoji Kimanin 200 Daga Najeriya

Ma’aikatar Tsaron Amurka, Pentagon, na shirin janye kimanin sojojin Amurka 200 daga Najeriya, watanni bayan tura su kasar domin taimakawa wajen yaki da kungiyoyin ’yan ta’adda. Rahotanni sun ce matakin na iya kawo karshen wani aikin hadin gwiwa da jami’an Amurka suka bayyana a matsayin abin da zai iya zama abin koyi ga ayyukan sojin Amurka a nan gaba a nahiyar Afirka. An tura sojojin Amurkan zuwa arewa maso gabashin Najeriya a watan Fabrairu , makonni kadan bayan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soki Najeriya kan abin da ya bayyana a matsayin gazawar kasar wajen kare Kiristoci daga hare-haren

Yan Sanda Sun Kama Likitoci Biyu Kan Zargin Safarar Mutane Da Cire Ƙoda A Nasarawa

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta kama wasu mutane huɗu da ake zargi da hannu a wata ƙungiyar safarar mutane da kuma cire sassan jikin bil’adama ba bisa ƙa’ida ba a Jihar Nasarawa. Waɗanda aka kama sun haɗa da Emmanuel Ode , mai shekaru 23; Dakta Benjamin Oyime , mai shekaru 48, likitan ƙoda a Wellington Hospital da ke Life Camp, Abuja; Dakta Daniel Otukpa , mai shekaru 53, likitan ƙoda kuma Mukaddashin Daraktan Ayyukan Kula da Lafiya na asibitin; da David Idoko , mai shekaru 25. Jami’an Special Tactical Squad ne suka kama mutanen a yayin wani samame na musamman da suka gudanar a ranar 19 ga Ag

Shettima Ya Tashi Zuwa Angola Don Wakiltar Tinubu A Taron AU

Mataimakin Shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya tashi daga Abuja zuwa Luanda, babban birnin Angola, domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron shugabannin ƙasashen Tarayyar Afirka (AU) na musamman karo na 21. Sanarwar da mai taimaka wa Mataimakin Shugaban Ƙasar kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, ya fitar, ta ce taron zai mayar da hankali ne kan hanyoyin warware rikice-rikice da kuma samar da zaman lafiya mai ɗorewa a nahiyar Afirka. Ana sa ran Mataimakin Shugaban Ƙasar zai gana da sauran shugabannin Afirka domin tattauna manyan ƙalubalen tsaro da nahiyar ke fuskanta, ta

Oluremi Tinubu Ta Bukaci ’Yan Najeriya Su Rungumi Zaman Lafiya da Tausayi a Maulidi

Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya, Oluremi Tinubu, ta buƙaci Musulman ƙasar da su yi koyi da rayuwa da koyarwar Annabi Muhammad (S.A.W) yayin da suke bikin Maulidin bana. A cikin saƙon taya murna da ta fitar domin zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W), Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ce bikin na ɗauke da muhimman darussa da suka haɗa da tausayi, yafiya da kuma zaman lafiya tsakanin al’umma. Ta taya al’ummar Musulmi murna tare da yi musu fatan alheri, inda ta shawarce su da su rungumi kyawawan ɗabi’un da Annabi Muhammad (S.A.W) ya koyar, tare da tabbatar da zaman lafiya a gidajensu, al’u

Zan tabbatar da cewa kowane yaro a jihar ya samu damar zuwa makaranta - Gwamna Jihar Jigawa

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa kowane yaro a jihar ya samu damar zuwa makaranta. Namadi, ya bayyana haka ne yayin ƙaddamar da rabon kayan tallafin karatu ga ɗalibai mata a makarantun sakandare da na gaba da sakandare a garin Jahun. Ya ce shirin zai taimaka wajen ƙara yawan ɗaliban da ke zuwa makaranta, musamman ’yan mata, tare da rage yawan masu daina zuwa makaranta. Gwamnan ya ce ilimi na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba, domin yana da muhimmanci wajen gina makomar jihar. A ƙarƙashin shirin, gwamnati za ta raba tufafin m

Jihar Imo Ta Yi Tiyatar Mutum-Mutumi Ta Farko a Najeriya

Jihar Imo ta samu gagarumar nasara a fannin kiwon lafiya, bayan da aka kammala tiyatar da aka yi da taimakon na’urar mutum-mutumi a karon farko a Specialist Hospital da ke Umuguma, Owerri. Tawagar ƙwararrun likitoci ’yan Najeriya da na ƙasashen waje ce ta gudanar da tiyatar, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Kingsley Ekwueme, wani ƙwararren likitan tiyatar mutum-mutumi da ke aiki a Birtaniya, kuma ɗan asalin Jihar Imo. Da yake magana da manema labarai a cibiyar Imo Robotics and Oncology Centre (IROC) , inda aka gudanar da aikin, Farfesa Ekwueme ya bayyana tiyatar a matsayin “cikakkiyar nasara.” Ya

EFCC ta janye karar da ta shigar kan Maryam Shehu bisa zargin bata suna

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta janye karar da ta shigar kan Maryam Isah Shehu da Abubakar Shuraim Abdulhamad, waɗanda aka gurfanar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin aikata laifukan yanar gizo da kuma yaɗa bayanan da hukumar ta ce suna da illa ga mutuncinta. An gurfanar da mutanen biyu ne ranar Alhamis, 20 ga watan Agustan 2026, a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, kan tuhume-tuhumen da suka shafi cin zarafi da bibiyar mutum ta kafafen intanet, wato cyberstalking. A cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na EFCC, Del

Gwamnatin Tarayya ta yi gargadin ambaliyar ruwa a jihohi 33

Gwamnatin Tarayya ta bayar da gargadin kwanaki bakwai kan yiwuwar fuskantar babban haɗarin ambaliyar ruwa a jihohi 33 na Najeriya, daga ranar 19 zuwa 25 ga Agusta 2026 . Gwamnatin ta ce ana sa ran matakan ruwan koguna za su ci gaba da tashi , lamarin da ka iya haddasa ambaliyar ruwa a wurare daban-daban cikin wannan lokaci. Jihohin da aka bayyana suna cikin haɗarin ambaliyar sun haɗa da Kaduna, Neja, Taraba, Ondo, Oyo, Rivers, Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Benue, Borno da Cross River . Sauran su ne Delta, Ebonyi, Edo, Enugu, Gombe, Imo, Jigawa, Kogi, Kwara, Nasarawa, Lagos, Ogun,

Shin kunsan ina makudan kudaden tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ke samu suke tafiya?

Gwamnatin Tarayya tace ta kashe Naira tiriliyan 9.39 wajen karin mafi karancin albashi da sauran alawus-alawus ga ma'aikatan gwamnati tsakanin Yuni 2023 da Disamba 2025. Ministan Kudi, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai kan sakamakon gyare-gyaren tattalin arzikin Najeriya da aka yada a gidan talabijin na Channels. Oyedele ya ce a cikin watanni 31, gwamnati ta samu karin albarkatun kudi na Naira tiriliyan 20.4 daga kudaden da aka samu bayan cire tallafin man fetur, karin kudaden shiga na cikin gida da kuma karin bashi. Sai dai ya ce ba a bar kudaden ba tare da yin amf

Kotun Cape Town Ta Dage Hukunci Chidinma Adetshina

Kotun Cape Town a Afirka ta Kudu ta dage yanke hukunci kan shari’ar Chidinma Adetshina, ‘yar asalin Najeriya kuma tsohuwar sarauniyar kyau, zuwa ranar 27 ga Fabrairu 2027 . Shari’ar ta shafi ƙalubalen da Adetshina ke yi kan matakin hukumomin Afirka ta Kudu na tsare ta da kuma yunƙurin fitar da ita daga ƙasar. A watan Yuni ne hukumomi suka kama Chidinma bayan ta sake shiga Afirka ta Kudu ta kan iyakar ƙasar da Mozambique. Batun ya samo asali ne daga takaddamar da ta kunno kai kan matsayin ƙasarta da kuma halaccin takardun da take amfani da su wajen zama a Afirka ta Kudu. An haifi Chidinma a Afi

’Yan sanda sun kama mutum kan zargin satar ƙarafunan digar jirgi a Bauchi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wani mutum mai suna Abubakar Sanusi bisa zargin hannu a satar ƙarafunan digar jirgi. Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Nafiu Habib, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa. Sanarwar ta ce jami’an ’yan sanda sun samu bayanan sirri game da satar ƙarafunan digar jirgin a ranar 17 ga Agustan 2026 , inda suka bi sawun kayan zuwa wani gida da ke unguwar Doya . Rundunar ta ce jami’anta sun samu nasarar ƙwato ƙarafunan digar jirgin tare da kama Abubakar Sanusi, wanda ake zargi da hannu a satar. A halin yanzu, ’yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike domin

Tsofaffin ’yan sanda a Adamawa sun yi alkawarin taimakawa wajen inganta tsaro

Ƙungiyar Tsofaffin Jami’an ’Yan Sandan Najeriya (NARPON), reshen Jihar Adamawa, ta yi alkawarin amfani da gogewarta wajen taimakawa wajen inganta tsaro da daƙile aikata laifuka a jihar. Jami’in Hulɗa da Jama’a na ’Yan Sanda shiyya ta 3, SP Aminu Umar Bashir, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa. Sanarwar ta ce Shugaban NARPON reshen Adamawa, ACP Dominic Yadubiya mai ritaya, ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci tawagar ƙungiyar zuwa ziyarar aiki a hedikwatar ’Yan Sanda ta shiyya ta 3 da ke Yola. Yadubiya ya ce tsofaffin jami’an za su yi amfani da ƙwarewa da ilimin da suka samu a lokacin da s

’Yan takarar shugaban ƙasa a Najeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Jam’iyyu da ’yan takarar shugaban ƙasa a Najeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta farko a Abuja, yayin da ake shirye-shiryen fara yaƙin neman zaɓen shekarar 2027. Yarjejeniyar ta ƙunshi alƙawarin gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana, tare da kauce wa kalaman tunzura jama’a, tashin hankali da duk wani mataki da ka iya kawo cikas ga tsarin zaɓe. Daga cikin ’yan takarar da suka halarci taron akwai Peter Obi na NDC, Donald Duke na PRP da Omoyele Sowore na African Action Congress (AAC) . Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Sanata Barau Jibrin, da wasu manyan

EFCC ta gurfanar da mutum kan zargin damfarar maniyyatan Haji N56.4m

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta gurfanar da wani mutum mai suna Lawal Babale Musa a gaban Babbar Kotun Jihar Oyo da ke Ibadan, bisa zargin damfarar wasu maniyyatan aikin Hajji kuɗi har Naira miliyan 56.49. EFCC ta gurfanar da Musa kan tuhume-tuhume 57 da suka shafi zargin sata, jabun takardu da kuma amfani da takardun bogi. Hukumar ta ce mutum 10 na daga cikin waɗanda ake zargin Musa ya karɓi kuɗaɗensu, inda jimillar kuɗin da ake zargin ya karɓa ta kai N56,491,000 tsakanin watan Nuwamban 2022 da Yulin 2024. A cewar EFCC, Musa ya riƙa gabatar da kansa ga waɗanda ya ka

An ƙaddamar da ƙungiyar Bajju UK & Europe domin kare al’ada da harshen Jju

An ƙaddamar da wata ƙungiyar Bajju UK & Europe a birnin Landan na Birtaniya, da nufin kare al’adu, harshen Jju da kuma ɗabi’un al’ummar Bajju da ke zaune a Birtaniya da sauran ƙasashen Turai. Rahotannin ƙaddamarwar sun tabbatar da cewa taron ya haɗa ’yan Bajju daga Birtaniya da kuma wasu da suka zo daga Najeriya. Al’ummar Bajju, waɗanda ke zaune musamman a kudancin Jihar Kaduna, suna magana da harshen Jju. Wani bincike kan harshen ya bayyana Jju a matsayin harshen Bajju, yayin da Kajju ke nufin ƙasar Bajju. Ƙungiyar ta ce ɗaya daga cikin manyan manufofinta ita ce tabbatar da cewa matasan Bajju

’Yan sandan Kebbi sun kama matashiya mai shekaru 19 kan zargin satar jariri

Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta kama wata matashiya mai shekaru 19, Khadija Ibrahim, bisa zargin satar wani jariri da aka haifa a Zuru tare da kai shi wajen mijinta, tana mai cewa ɗansu ne. A cewar rundunar, lamarin ya faru ne a ranar 23 ga Yuli, 2025, jim kaɗan bayan mahaifiyar jaririn, Fatima Muhammad, ta haife shi. Ana zargin Khadija ta nemi taimakawa sabuwar mahaifiyar wajen samo mata ruwan zafi, amma ta yi amfani da damar wajen ɗauke jaririn tare da guduwa da shi. Binciken ’yan sanda ya nuna cewa ana zargin matashiyar ta fuskanci matsin lamba na zamantakewa da na tunani sakamakon rash