Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wani mutum mai suna Abubakar Sanusi bisa zargin hannu a satar ƙarafunan digar jirgi.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Nafiu Habib, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.
Sanarwar ta ce jami’an ’yan sanda sun samu bayanan sirri game da satar ƙarafunan digar jirgin a ranar 17 ga Agustan 2026 , inda suka bi sawun kayan zuwa wani gida da ke unguwar Doya .
Rundunar ta ce jami’anta sun samu nasarar ƙwato ƙarafunan digar jirgin tare da kama Abubakar Sanusi, wanda ake zargi da hannu a satar.
A halin yanzu, ’yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike domin gano tare da kama sauran mutanen da ake zargin suna da hannu a aikata laifin.
Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda bincike ya tabbatar da hannu a lamarin.
