Kungiyar kwallon kafa ta kasar Portugal ta tabbatar da jerin sunayen 'yan wasanta da zasu fafata a gasar cin kofin duniya ta FIFA na shekarar 2026 mai zuwa, inda Cristiano Ronaldo ke shirin kafa tarihin fitowa karo na shida a gasar.
Dan wasan gaba mai shekaru 41 yana ci gaba da nuna juriya da bajinta a matakin kasa da kasa, inda yake jagorantar tawagar da ke cike da kwararrun 'yan wasa masu fasaha da gogewa.
Dama can ana fakar idon ganin sunansa a jeri, amma duk da haka wannan ya zama wani lokaci na tarihi a duniyar kwallon kafa, domin babu wani namiji da taba buga gasar cin kofin duniya har sau shida.
Kamar yadda kafar yada labarai ta BBC Sport ta ruwaito a ranar Talata, babban mai horar da 'yan wasan kasar, Roberto Martinez, ya magantu game da yadda zaben 'yan wasan ya taba masa zuciya, musamman ma yadda suka tuna da tsohon dan wasan kasar, Diogo Jota.
“Shi ne karfinmu, kuma abin farin cikinmu. Rasa Diogo wani lokaci ne mai wahala da ba za mu taba mantawa da shi ba, amma washegari sai ya zama wajibi a kanmu baki daya mu yi yaki domin tabbatar da mafarkin Diogo da kuma misalin da ya saba nunawa a kungiyarmu ta kasa.”
Ya kara da cewa: “Ruhin Diogo Jota, karfinsa, da kuma misalinsa su ne za su zama mana ƙarin kwarin gwiwa a koda yaushe.”
Kasancewar Ronaldo na ci gaba da zama jigo a burukan da Portugal ke son cimmawa, inda ake sa ran Martínez zai raba lokutan buga wasansa cikin katsantsan a tsakanin matasa da tsofaffin 'yan wasan kungiyar.
Tawagar ta kuma hada da Bruno Fernandes, Bernardo Silva, Rúben Dias, João Félix, Rafael Leão, da Gonçalo Ramos.
Wannan zabe ya sake bude wani sabon shafi na babbar gasa ga Ronaldo, wanda dama shi ne ke rike da tarihin maza na yawan buga wasanni da kuma zura kwallaye a matakin kasa da kasa.
Kasar Portugal za ta yi kokarin amfani da wannan tsara na fitattun 'yan wasa masu hazaka domin samun nasara a gasar cin kofin duniya, inda ake sa ran za su yi nisa sosai a gasar.
Jerin Sunayen 'Yan Wasan Portugal na Gasar Cin Kofin Duniya:
- Masu Tsaron Gida: Diogo Costa (Porto), Jose Sa (Wolves), Rui Silva (Sporting), Ricardo Velho (Genclerbirligi).
- Masu Tsaron Baya: Diogo Dalot (Manchester United), Matheus Nunes (Manchester City), Ruben Dias (Manchester City), Nelson Semedo (Fenerbahce), Joao Cancelo (Barcelona), Nuno Mendes (Paris St-Germain), Goncalo Inacio (Sporting), Renato Veiga (Villarreal), Tomas Araujo (Benfica).
- Masu Bugawa a Tsakiya: Ruben Neves (Al-Hilal), Samu Costa (Mallorca), Joao Neves (Paris St-Germain), Vitinha (Paris St-Germain), Bruno Fernandes (Manchester United), Bernardo Silva (Manchester City).
- Masu Wasan Gaba: Cristiano Ronaldo (Al-Nassr), Joao Felix (Al-Nassr), Francisco Trincao (Sporting), Francisco Conceicao (Juventus), Pedro Neto (Chelsea), Rafael Leao (AC Milan), Goncalo Guedes (Real Sociedad), Goncalo Ramos (Paris St-Germain).