Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce ta kama wasu mutane bakwai da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, tare da kwato kwayoyi daban-daban 5,916 da tubalan tabar wiwi guda biyar.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, SP Shiisu Lawan Adam, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, a madadin Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Tijjani Murtala.
A cewar sanarwar, an gudanar da samamen ne bisa sahihan bayanan sirri a yankunan rundunonin ’yan sanda na Kazaure, Gumel, Miga, Dutse, Sundumina, Taura, Babura, Ringim, Sara da Aujara.
Rundunar ta ce daga cikin abubuwan da jami’anta suka kwato akwai Exol, Tramadol, D5, Diazepam, Taramol, Rubber Solution da Pregabalin, baya ga tabar wiwi da sauran miyagun kwayoyi.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Yahaya Ibrahim, mai shekaru 35, daga Darai a ƙaramar hukumar Jahun; Adamu Ya’u, mai shekaru 33, daga Jamaga a ƙaramar hukumar Miga; da Musa Musa, mai shekaru 22, wanda aka fi sani da Alili Boss, daga Nasarawa Jalo Quarters a Gumel.
Sauran waɗanda aka kama su ne Sani Kabiru, mai shekaru 35, daga ƙaramar hukumar Ingawa ta Jihar Katsina; Hashimu Haladu, mai shekaru 40, daga Nafara, Sundumina, ƙaramar hukumar Birnin Kudu; Mustapha Kabiru, mai shekaru 22, daga Katutu Quarters, Ringim; da Sani Harisu, mai shekaru 25, daga Tsangaya Quarters, Sara, ƙaramar hukumar Gwaram.
Rundunar ta ce an gudanar da binciken farko kan waɗanda ake zargin, kafin a gurfanar da su gaban kotunan da suka dace domin fuskantar shari’a bisa tanadin doka.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jigawa, CP Tijjani Murtala, ya yaba wa jami’an rundunar bisa jajircewarsu wajen yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da shaye-shaye a jihar.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da amfani da bayanan sirri wajen gudanar da ayyukan tsaro, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro domin dakile laifuka da tarwatsa hanyoyin safarar miyagun ƙwayoyi.
Kwamishinan ya kuma gargadi masu safarar miyagun ƙwayoyi da sauran waɗanda ke da hannu wajen samarwa, rarrabawa ko safarar su cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen gurfanar da su gaban kotu.
Ya buƙaci iyaye, shugabannin al’umma, malamai, matasa da sauran jama’a da su riƙa bai wa ’yan sanda sahihan bayanai kan masu safarar miyagun ƙwayoyi da sauran masu aikata laifuka a cikin al’ummominsu.