Rundunar 'yan sandan jihar Kogi ta bayyana cewa ta kama wani mutum mai shekaru 52 da kulli 339 na haramtattun kwayoyi da ake zargi wiwi ce (ganyen taba wiwi) a garin Kabba, da ke karkashin Karamar Hukumar Kabba/Bunu a jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Naziru Kankarofi, ya shaida wa manema labarai a wani taron manema labarai da aka gudanar a babban sakatariyar rundunar da ke Lokoja ranar Talata cewa, an yi kamun ne a ranar 9 ga watan Mayu, 2026, da misalin karfe biyu na rana (1400hrs) ta hanyar yin amfani da bayanan sirri, dabarun tsayar da motoci don bincike, da kuma matakan riga-kafin aikata laifuka.

“A ranar 9 ga watan Mayu, 2026, da misalin karfe 14:00 na rana, jami'an rundunar 'yan sanda ta shiyyar Kabba (Area Command), yayin da suke gudanar da aikin binciken ababen hawa na yau da kullum, sun tsayar da wata mota kirar Honda Pilot Jeep mai lambar rajista LSD 456 GE. Wani mutum mai suna Chris Amos na miji, mai shekaru 52 ne ke tuka motar, yayin da wani Bilat Joseph na miji ke zaune a matsayin fasinja.

“Bayan gudanar da bincike mai zurfi a cikin motar, jami’an sun gano kulli dari uku da talatin da tara (339) na wasu abubuwa da ake kyautata zargin wiwi ce da aka boye a cikin motar,” in ji kwamishinan.

Ya kara da cewa, binciken farko-farko ya nuna cewa wadanda ake zargin sun amshi kayan ne daga garin Ado-Ekiti da ke jihar Ekiti bisa umarnin wani mutum da aka bayyana da sunan "Alhaji," wanda har yanzu ba a san cikakken ko wanene shi ba da kuma inda yake, kuma a halin yanzu ana tsaka da gudanar da bincike a kansa.

"Wadanda ake zargin sun kuma bayyana cewa an yi nufin kai waɗannan haramtattun kwayoyin ne zuwa birnin Yola da ke jihar Adamawa," in ji Kankarofi.