Hukumar Tara Haraji ta Najeriya (NRS) ta yi gargadin cewa ci gaba da samun gibin haraji, jinkirin tura kudaden haraji da kuma rashin bin ka’idoji daga wasu hukumomin gwamnati da jihohi na iya kawo cikas ga kudirin tara kusan naira tiriliyan 40 a shekarar 2026.
Hukumar ta bayyana hakan ne yayin wani taron kasa kan karfafa bin sabbin dokokin haraji da aka gudanar a Abuja, inda jami’an gwamnatin tarayya, jihohi, ma’aikatu da hukumomin tara kudaden shiga suka tattauna hanyoyin bunkasa tattara haraji.
Da take jawabi a wajen taron, Daraktar kula da manyan masu biyan haraji da bangaren gwamnati na hukumar, Amina Ado, ta ce hukumar ta gano manyan gibi wajen tura kudaden haraji yayin bincike da sa ido da take gudanarwa.
A cewarta, rashin bin ka’idojin biyan haraji yadda ya kamata na iya rage kudaden shiga da gwamnati ke bukata domin gudanar da ayyukan ci gaba da samar da muhimman ayyuka ga al’umma.