Farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya ragu zuwa kusan dala 90 kan kowace ganga, bayan da Amurka da Iran suka dakatar da hare-haren da suke kai wa juna domin bai wa tattaunawar diflomasiyya damar ci gaba.

A ranar Litinin, farashin Brent Crude ya ragu da kashi 6.76% zuwa dala 90.24 kan kowace ganga, yayin da US West Texas Intermediate (WTI) ya fadi da kashi 6.04% zuwa dala 83.92 kan kowace ganga.

Rahotanni sun ce faduwar farashin ta biyo bayan dakatar da hare-haren da ɓangarorin biyu suka yi a ƙarshen mako, bayan kusan makonni biyu ana musayar hare-hare.

Jakadan Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya, Mike Waltz, ya bayyana cewa Shugaba Donald Trump ya dakatar da hare-haren ne domin bai wa tattaunawar diflomasiyya damar samun ci gaba. A nasa ɓangaren, wani babban jami'in gwamnatin Iran ya shaida wa Reuters cewa ƙasar za ta dakatar da hare-harenta matuƙar Amurka ta ci gaba da tsayawa kan wannan matsaya.

A ranar 23 ga Yuli, farashin danyen mai ya taɓa haura dala 100 kan kowace ganga bayan rahotannin hare-hare kan wasu jiragen ruwa a Tekun Red Sea.

Karuwar farashin danyen mai ta yi tasiri a Najeriya, inda farashin man fetur ya ƙaru. A ranar 23 ga Yuli, Matatar Dangote ta ƙara farashin fetur daga Naira 1,075 zuwa Naira 1,215 kan kowace lita, tare da ci gaba da sayar da fetur a cikin kuɗin naira.

Haka kuma, tun ranar 16 ga Yuli, masu shigo da man fetur sun bayyana shirin ƙara farashin fetur a ma'ajiyun ajiya daga Naira 1,230 zuwa Naira 1,350 kan kowace lita.