Lauyoyin da ke aiki a Ma'aikatar Shari'a ta Jihar Kwara sun fara yajin aiki na sai baba-ta-gani, sakamakon zargin rashin biyan wasu alawus da suke bin gwamnatin jihar, tare da neman daidaita albashi da sauran haƙƙoƙinsu da na alkalan kotunan majistare.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Law Officers Association of Nigeria (LOAN) reshen Jihar Kwara ce ta sanar da fara yajin aikin, inda ta umarci dukkan mambobinta su dakatar da ayyukansu na hukuma har sai an biya buƙatunsu.
Shugaban riƙo na ƙungiyar, Kehinde Ayorinde, ya ce yajin aikin zai ci gaba ne har sai gwamnatin jihar ta ɗauki matakan da suka dace domin warware matsalolin da suka gabatar.
A cewar ƙungiyar, tana neman a biya ragowar alawus na kayan ɗaki na shekarar 2020, da kuma alawus na rigar aiki na shekarun 2024, 2025 da 2026.
Haka kuma, ƙungiyar na buƙatar gwamnatin jihar ta aiwatar da daidaita albashi da sauran sharuɗɗan aiki na lauyoyin gwamnati da na alkalan kotunan majistare.
LOAN ta bayyana cewa ta ɗauki wannan mataki ne bayan wa'adin kwanaki bakwai da ta bai wa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ƙare ba tare da an warware matsalolin ba, duk da ƙoƙarin tattaunawa da aka yi da gwamnatin jihar.