Gwamnatin Najeriya, ta hannun Ofishin Jakadancinta da ke Johannesburg, ta yi Allah wadai da kisan wani ɗan ƙasar, Ibeh Chika Simon, wanda ya rasa ransa yayin wani samamen da 'yan sandan Afirka ta Kudu suka kai a yankin Bellville da ke Cape Town a ranar 23 ga Yuli.

A cikin wata sanarwa, jakadancin ya ce mutuwar marigayin ta faru ne a yanayi da ke haifar da tambayoyi masu yawa. Haka kuma, wani ɗan Najeriya, Egwabor Patrick Chuks, ya samu munanan raunuka bayan harbin bindiga da aka yi masa a lokacin samamen.

Jakadancin ya bayyana matuƙar damuwarsa kan lamarin, yana mai zargin jami'an tsaron da amfani da ƙarfi fiye da kima, tare da danganta wannan lamari da abin da ya ce na ci gaba da kashe-kashen da ba a warware ba da kuma zargin cin zarafin baƙi a Afirka ta Kudu.

Najeriya ta buƙaci hukumomin Afirka ta Kudu da su gudanar da bincike cikin gaggawa, adalci da gaskiya, tare da hukunta duk wanda bincike ya nuna yana da hannu a lamarin.

A nata ɓangaren, Kwamitin Ministoci Kan Harkokin Hijira na Afirka ta Kudu ya tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike kan abin da ya faru.

Ministar Shari'a ta Afirka ta Kudu, Mmamoloko Kubayi, ta ce yayin samamen, wasu mutane sun yi turjiya ga jami'an tsaro, yayin da wasu baƙi suka hana su gudanar da aikinsu. Ta ƙara da cewa za a bayyana sakamakon binciken da zarar an kammala shi.

Ministar ta kuma bayyana damuwar gwamnati kan hare-haren da ake kai wa baƙi, tana mai cewa an kama mutane bakwai da ake zargi da hannu a irin waɗannan hare-haren.