Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Human Rights Watch (HRW) ta yi gargaɗin cewa ayyukan hako mai da kamfanin Perenco ke gudanarwa a yankin Muanda da ke lardin Kongo a Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC), na iya zama barazana ga lafiyar jama'a da kuma muhalli.
A cewar rahoton HRW, hayaƙin da kamfanin ke fitarwa da kuma ƙona tarkacen mai sun gurɓata ingancin iska, yayin da malalar mai daga rijiyoyi da bututun mai ta gurɓata koguna da ƙasa.
Mazauna yankunan sun ce suna fama da matsalolin numfashi, ciwon ƙirji da tashin zuciya, kuma suna danganta waɗannan matsaloli da ayyukan kamfanin.
Sai dai kamfanin Perenco ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa rahoton na ɗauke da kura-kurai. Kamfanin ya ce ya zuba jari wajen rage gurɓacewar muhalli, tare da tallafa wa ayyukan kiwon lafiya. Haka kuma ya bayyana cewa ya dakatar da fitar da hayaƙin gas a wurare sama da 200, kuma yana aiki tare da hukumomin Kongo wajen inganta matakan kare muhalli.
A nata ɓangaren, gwamnatin Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta umarci a gudanar da binciken muhalli kan ayyukan kamfanin tun ƙarshen shekarar 2024, amma har yanzu ba ta fitar da sakamakon binciken ba.
Human Rights Watch ta buƙaci gwamnatin Kongo da ta bayyana sakamakon binciken tare da ɗaukar matakan da suka dace domin kare lafiyar al'umma da muhalli.
Kamfanin Perenco, wanda shi ne kaɗai mai hako danyen mai a Kongo, na gudanar da ayyukansa a kan tudu da kuma a tekun bakin gaɓar ƙasar mai tsawon kilomita 37.