Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya haƙura da neman wa'adi na biyu a zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa shugaban ya gaji kuma ba shi da ƙarfin da zai iya magance matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro da ƙasar ke fuskanta.
A wata hira da gidan talabijin na Channels Television, Obi ya ce Tinubu na yanzu ba irin shugaban da ya yi mulkin Jihar Legas ba ne, yana mai zargin gwamnatinsa da gaza shawo kan matsalolin talauci, yunwa da rashin tsaro.
Obi ya ce rahotannin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sun nuna cewa miliyoyin 'yan Najeriya na fama da talauci da ƙarancin abinci, amma a cewarsa, maimakon mayar da hankali kan waɗannan ƙalubale, ana yawan tattauna batutuwan siyasa.
Ya ƙara da cewa ba za a iya magance matsalar rashin tsaro yadda ya kamata ba sai an rage talauci, an zuba jari sosai a fannin ilimi, tare da samar da ayyukan yi ga matasa.
Duk da yabon da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi wa gwamnatin Tinubu kan ƙoƙarinta a fannin tsaro, Obi ya ce matakan da ake ɗauka a halin yanzu ba su isa ba.
Ya jaddada cewa burinsa ba wai zama shugaban ƙasa kaɗai ba ne, illa ganin Najeriya ta samu ci gaba, zaman lafiya da kyakkyawar rayuwa ga al'ummarta.