Shugaban Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, Hon. Anas Muƙhtar Danmaliki, ya jagoranci bikin raba takardun shaidar ɗaukar aiki ga mutane 137 da Gwamnatin Jihar Kano ta ɗauka aiki ƙarƙashin shirin BESDA (Better Education Service Delivery for All).


Da yake jawabi a wajen taron, Hon. Danmaliki ya bayyana bikin a matsayin wani babban ci gaba ga al’ummar Dawakin Tofa, yana mai cewa ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma.


Ya ce shirin zai taimaka wajen samar wa matasa aikin yi tare da ƙarfafa harkar ilimi a faɗin ƙaramar hukumar.


Shugaban ƙaramar hukumar ya shawarci sabbin malaman da kada su ɗauki aikin a matsayin hanyar neman kuɗi kawai, yana mai jaddada cewa an ɗora musu amanar koyarwa da tarbiyyar yara.


Ya buƙace su da su kasance masu tsoron Allah, riƙon amana, jajircewa da gaskiya wajen gudanar da ayyukansu.


Haka kuma, Hon. Danmaliki ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa ci gaba da ba fannonin ilimi, lafiya da walwalar al’umma muhimmanci.


Ya tabbatar da cewa gwamnatin ƙaramar hukumar za ta ci gaba da mara wa gwamnatin jihar baya domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.


A nasa jawabin, Sakataren Ilimi na yankin, Farfesa Mamuna Mustapha, ya taya waɗanda suka samu aikin murna, tare da ƙarfafa musu gwiwa da su kasance masu ƙwazo da riƙon amana wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.


Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da shirin, Malam Idris Sale da Hassan Ado Wakili, sun bayyana farin cikinsu bisa samun aikin, tare da yin addu’ar Allah Ya ba su ikon gudanar da aikin koyarwa da tarbiyyar ɗalibai yadda ya kamata.


Bikin ya samu halartar Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, kansiloli zaɓaɓɓu da naɗaɗɗu, shugabannin sassa da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa a ƙaramar hukumar.