Gwamnatin Ghana ta sanar da cewa karin 'yan ƙasarta 1,000 da ke aiki a matsayin baƙin haure a Afirka ta Kudu za su fara komawa gida a ranakun Lahadi da Litinin, sakamakon ci gaba da zanga-zangar da ta rikide zuwa tashin hankali kan baƙin haure.

Tun da farko, hukumomin Ghana sun yi nasarar kwashe 'yan ƙasa 926 daga Afirka ta Kudu, yayin da gwamnatin ta yi Allah wadai da hare-haren da suka yi sanadin asarar rayuka a ƙasar.

A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Ghana ta fitar a daren Asabar, ta bayyana cewa jirage na musamman za su fara isa Ghana a ranakun Lahadi da Litinin domin dawo da sauran 'yan ƙasar. Ta ce wannan shi ne mataki na ƙarshe na shirin kwashe 'yan Ghana daga Afirka ta Kudu.

Shugaban Ghana, John Mahama, ya kuma yi kira ga Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) da ta sanya batun hare-haren ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu cikin ajandar taronta, yana mai zargin gwamnatin Pretoria da gaza ɗaukar isassun matakan dakile tashe-tashen hankulan.