Gwamnatin Jihar Sokoto ta bayyana cewa ba ta da wata alaƙa da wani mai sihiri da aka fi sani da suna Mai Shaho, bayan wani faifan bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta.

A cikin bidiyon, an ga mutumin yana binne bunsuru da rai tare da ikirarin cewa ɗan takarar gwamna na jam'iyyar ADC a jihar ba zai yi nasara ba.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama'a na Gidan Gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar, gwamnatin ta nesanta kanta da mutumin da kuma duk wani abu da ya shafi ayyukansa.

Sanarwar ta jaddada cewa gwamnatin jihar ba ta goyon bayan sihiri ko duk wani aiki da ya saɓa wa koyarwar addinin Musulunci.

"Jihar Sokoto jiha ce da galibin al'ummarta Musulmai ne, kuma mutanenta suna riƙe da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa, tare da bin tafarkin Mujaddadi Sheikh Usmanu Ɗanfodiyo. Saboda haka, Gwamnatin Jihar ba za ta amince da duk wani aiki da ya saɓa wa koyarwar Musulunci ba."

Gwamnatin ta kuma yi kira ga al'umma da su yi watsi da duk wani yunƙuri na danganta ta da irin waɗannan ayyuka.