Amurka da Iran sun mayar da martani mai kyau ga wata shawarar sasanci da ƙasashen Pakistan da Qatar suka gabatar domin kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu, inda rahotanni suka nuna cewa ɓangarorin biyu sun amince da amfani da tattaunawa da diflomasiyya wajen rage zaman ɗar-ɗar.

Kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito cewa shirin sasancin ya haɗa da komawa yanayin da ake ciki kafin ɓarkewar sabon rikicin da ya ɗauki kwanaki 17, tare da komawa teburin tattaunawa domin nemo mafita ta lumana.

Majiyoyi sun bayyana cewa an dakatar da hare-haren da Amurka da Iran ke kai wa juna na tsawon kwanaki biyu, bayan wata tawagar diflomasiyyar ƙasar Oman ta kai ziyara birnin Tehran.

Rahotanni daga kafofin yaɗa labarai na Amurka sun kuma nuna cewa Shugaba Donald Trump ya yanke shawarar dakatar da ƙarin hare-haren soji kan Iran a halin yanzu. Ita kuwa Iran ta ce ta dakatar da hare-harenta saboda manufarta ita ce mayar da martani kawai, ba ci gaba da yaƙi ba.

A halin yanzu, Pakistan da Qatar na ci gaba da jagorantar ƙoƙarin sasanci, inda suka bayyana dakatar da hare-haren a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa fata wajen samun zaman lafiya tsakanin ɓangarorin biyu.