Rundunar Operation FANSAN YAMMA ta ce ta ƙara zage damtse wajen ceto Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara, Alhaji Nura Umar Abdullahi, wanda wasu 'yan ta'adda suka yi garkuwa da shi a safiyar ranar 25 ga Yuli, 2026.

A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar, maharan sun kai hari gidan shugaban ƙaramar hukumar inda suka yi nasarar yin garkuwa da shi da wasu daga cikin iyalansa bayan sun yi galaba kan jami'an 'yan sanda da masu aikin sa-kai da ke gadinsa.

Bayan jin karar harbe-harbe, dakarun Operation FANSAN YAMMA sun garzaya wurin tare da bin sawun maharan, lamarin da ya kai ga musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.

Sanarwar ta ce sakamakon gaggawar da dakarun suka yi, maharan sun bar mutane biyar daga cikin iyalan shugaban ƙaramar hukumar, da suka haɗa da 'ya'yansa biyu, mahaifiyarsa, matarsa da wani ɗan uwansa, waɗanda aka yi nasarar ceto.

Sai dai maharan sun tsere da Shugaban Ƙaramar Hukumar zuwa cikin daji.

Rundunar ta kuma bayyana cewa harin ya yi sanadin mutuwar 'yan sanda biyu da ɗan kungiyar sa-kai guda ɗaya da suka yi ƙoƙarin kare shugaban. Haka kuma, wani farar hula ya rasa ransa, yayin da babban ɗan'uwan shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Bello Umar, ya samu raunuka.

Bayan harin, rundunar ta ƙaddamar da wani gagarumin samame na haɗin gwiwa tare da Rundunar 'Yan Sandan Najeriya, Hukumar DSS da kuma masu aikin sa-kai domin gano maboyar maharan da ceto shugaban cikin ƙoshin lafiya.

Operation FANSAN YAMMA ta tabbatar wa gwamnatin Jihar Zamfara da al'ummar jihar cewa tana amfani da dukkan hanyoyin da suka dace wajen ganin an ceto shugaban tare da cafke waɗanda suka aikata wannan ta'asa.

Rundunar ta kuma yi kira ga jama'a da su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin natsuwa, tare da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanan da za su taimaka wajen nasarar wannan aiki.