Dakarun Joint Task Force North West – Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 48 da aka yi garkuwa da su bayan gaggawar kai ɗauki sakamakon harin da 'yan ta'adda suka kai ƙauyen Magami da ke Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara, a safiyar ranar 26 ga Yuli, 2026.

A cewar wata sanarwa da Rundunar ta fitar, dakarun Sector 2 sun tashi kai tsaye bayan samun kiran gaggawa cewa wasu 'yan ta'adda da ke kan babura kusan 40 sun mamaye ƙauyen tare da tattara mazauna domin yin garkuwa da su zuwa cikin daji.

Da isar dakarun wurin, nan take suka fafata da maharan a wani mummunan artabu, lamarin da ya tilasta wa 'yan ta'addan tserewa tare da barin mutanen da suka yi garkuwa da su.

Sakamakon wannan samame, an yi nasarar ceto duka mutane 48 da aka sace.

Sai dai sanarwar ta ce mutum ɗaya ya rasa ransa a harin, yayin da wasu biyu suka samu raunukan harbin bindiga. An garzaya da su Babban Asibitin Kaura Namoda, inda suke ci gaba da karɓar magani.

Bayan kammala aikin ceto, dakarun sun ci gaba da sintiri a yankin domin hana sake kai wani hari da kuma tabbatar da tsaron al'umma.

Rundunar Operation FANSAN YAMMA ta yaba wa jajircewar dakarunta, tare da sake tabbatar da aniyarta na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al'ummar Arewa maso Yamma. Haka kuma ta yi kira ga jama'a da su ci gaba da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai domin ƙarfafa yaƙi da ta'addanci.