Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani Kwamitin Haɗin Gwiwar Ma'aikatu domin tsara Dokar Gyaran Harajin Ƙarin Daraja (VAT Modification Order) ta shekarar 2026, a wani muhimmin mataki na aiwatar da sabbin dokokin haraji na Najeriya.

Ministan Kuɗi kuma Ministan Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, ne ya rantsar da mambobin kwamitin, wanda aka ɗora wa alhakin nazarin tanade-tanaden da suka shafi kayayyaki da ayyukan da aka keɓe daga biyan VAT ko aka sanya musu harajin sifili (Zero-rated) ƙarƙashin Dokar Haraji ta Najeriya.

Ana kuma sa ran kwamitin zai gabatar da shawarwari kan yadda za a samar da tsari mafi sauƙi kuma mai inganci ga 'yan kasuwa da masu gudanar da harkokin haraji.

Kwamitin ya ƙunshi wakilai daga Ma'aikatar Kuɗi, Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Najeriya (Nigeria Revenue Service), Hukumar Kwastam ta Najeriya, Ma'aikatar Kasuwanci, Ƙungiyar Masana'antu ta Najeriya (MAN), Kwamitin Ba da Shawara Kan Haraji, da kuma Tax Justice and Governance Platform.

An bai wa kwamitin wa'adin mako shida domin gabatar da daftarin dokar gyaran VAT, sabon jadawalin kayayyaki da ayyukan da za a keɓe daga haraji, tare da rahoton shawarwarin da aka tattara daga masu ruwa da tsaki.