Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na mayar da Jami'ar Sojojin Najeriya da ke Biu (NAUB) ta zama cibiyar koyarwa ta ƙwarai wajen horar da jami'an soja da fararen hula.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Ministan Tsaro Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Leah Katung-Babatunde, ta fitar.

A cewar sanarwar, Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin mambobin Majalisar Gudanarwar jami'ar a hedikwatar Ma'aikatar Tsaro da ke Abuja. Ya tabbatar musu da ci gaba da ba jami'ar cikakken goyon baya, yana mai cewa NAUB na taka muhimmiyar rawa wajen samar da ƙwararrun ma'aikata masu ilimin fasaha da ƙwarewar aiki domin fuskantar sabbin ƙalubalen tsaro.

Sanarwar ta ƙara da cewa Ma'aikatar Tsaro za ta yi aiki tare da Rundunar Sojojin Najeriya domin tabbatar da cikakken amfani da kaso 30 cikin 100 na guraben shiga jami'ar da aka ware wa jami'an soja, domin cike gibin ƙwarewa a fannin tsaron ƙasa.

A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Gudanarwar Jami'ar, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya), ya yabawa Ministan Tsaro bisa jagorancinsa da hangen nesansa, yana mai cewa gudunmawar da yake bayarwa na ci gaba da ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya.