Hukumomi a kudu maso yammacin Faransa sun umarci karin mutum 55,000 da su fice daga gidajensu a yankunan da ke kusa da birnin Bordeaux, sakamakon ci gaba da bazuwar mummunar gobarar daji.

A halin yanzu, jimillar mutum kusan 250,000 aka umarta su bar gidajensu domin kare rayukansu daga barazanar gobarar.

Firaministan Faransa ya bayyana cewa iska mai ƙarfi da tsananin zafi na ci gaba da ƙara tsananta gobarar, lamarin da ke kawo cikas ga ƙoƙarin jami'an kashe gobara na shawo kan lamarin.

Sai dai rahotannin farko da aka fitar a ranar Asabar sun nuna cewa ƙarfin gobarar ya fara raguwa a wasu yankuna, duk da cewa har yanzu ana ci gaba da sanya ido kan halin da ake ciki.

A wani mataki na gaggawa, gwamnatin Faransa ta tura wani katafaren jirgin saman soji na dakon kaya karo na farko domin yayyafa sinadaran kashe gobara a wuraren da gobarar ta fi ƙamari a kusa da birnin Bordeaux.