Dan Majalisar Wakilan Amurka mai wakiltar jihar Michigan, John James, ya bukaci gwamnatin Najeriya ta saki jagoran haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ko kuma ta fuskanci yiwuwar rage tallafin da Amurka ke bai wa ƙasar.
James ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisar wakilan Amurka, inda ya bukaci a sake gudanar da shari'ar Kanu bisa kundin tsarin mulkin Najeriya da ƙa'idodin kare haƙƙin ɗan Adam na ƙasa da ƙasa. Ya kuma yi zargin cewa ana tauye haƙƙin Kiristoci a Najeriya.
Dan majalisar ya ce idan ba a saki Kanu ba, ya kamata Amurka ta sake duba tallafin kuɗaɗen da take bai wa Najeriya.
A martaninsa, mai magana da yawun IPOB, Emma Powerful, ya yabawa wannan kira, yana mai cewa hakan na nuna ƙarin hankalin ƙasashen duniya kan shari'ar Kanu.
Nnamdi Kanu na zaman gidan yari bayan da aka yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai a watan Nuwamban 2025 bisa samunsa da laifukan ta'addanci, kuma har yanzu ana jiran sakamakon ƙarar da ya ɗaukaka.