Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal, ya ce tikitin takarar shugaban ƙasa na haɗin gwiwa tsakanin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso na da damar lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 fiye da idan kowannensu ya tsaya takara daban.


Lawal ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Symfoni TV, wadda aka fitar a ranar Asabar.


A cewarsa, idan Obi da Kwankwaso suka haɗa kai a tikiti ɗaya, suna da kusan kashi 70 cikin 100 na damar samun nasara, yayin da ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu kusan kashi 50 cikin 100, sannan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ba zai samu nasara ba.


“Peter Obi zai yi ƙoƙarin yi wa kowa adalci. Peter Obi zai yi abin da ya dace. Peter Obi da Kwankwaso, ku lura, ina haɗa su ne. Ina haɗa su. Idan suka tsaya daban, hakan zai zama bala’i. Amma idan suka haɗa kai, a ma’aunina zan ba su kusan kashi 70 cikin 100. Bola kuma kashi 50. Atiku kuwa sifili.”




Lawal ya kuma jaddada cewa Atiku ba zai lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 ba.


“Tabbas Atiku zai sha kaye. Zai sha kaye, kuma ina addu’ar ya sha kaye. Ba ni kaɗai nake da wannan ra’ayi ba, kuma zai sha kaye.”


Kalaman Lawal na zuwa ne bayan saɓanin da ya shiga da Atiku bayan ficewarsa daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).


Tsohon SGF ɗin ya sha zargin cewa zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, wanda ya bai wa Atiku tikitin takara, ya cika da kura-kurai da rashin gaskiya, zarge-zargen da jam’iyyar ba ta amince da su a hukumance ba.