Iran ta gayyaci jami'an diflomasiyyar Ukraine bayan da ta zargi Kyiv kai harin bam kan wani jirgin ruwanta a Tekun Caspian, lamarin da ya yi sanadin mutuwar ma'aikacin jirgin ruwa ɗaya tare da raunata wani.
Cikin wata sanarwa ranar Asabar, Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da harin da Ukraine ta kai wa wani jirgin ruwan kasuwancin ƙasar a Tekun Caspian.
Ukraine dai ta ce tana kai hari kan jiragen ruwan Rasha da ke ɗauke da kayyayyakin soja masu alaka da Iran.
Shugaba Volodymyr Zelenskyy ya ce Rasha tana taimaka wa Iran a yakin Gabas ta Tsakiya.
A duk tsawon yakin Ukraine na sama da shekaru uku, Kyiv ta fuskanci jiragen sama marasa matuki kirar Iran da Moscow ke amfani da su. Yayin da Ukrain ta taimaka kwarewarta na yankin Gabas ta Tsakiya dake fuskantar hare-haren Iran garkuwar tare jiragen sama marasa matuki.