Kotun Sauraren Kararrakin Wasanni ta Duniya (CAS) ta sanya 8 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta fara sauraren ƙarar da Senegal ta ɗaukaka kan hukuncin da ya ƙwace mata kofin gasar AFCON 2025.

Tun farko, Senegal ce ta doke Morocco da ci 1-0 a wasan ƙarshe na gasar da aka kammala a watan Janairu. Sai dai daga bisani Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta sauya hukuncin, tare da ayyana Morocco a matsayin zakara bayan ta bai wa Senegal hukuncin shan kashi da ci 3-0.

Lamarin ya samo asali ne bayan 'yan wasan Senegal sun fice daga filin wasa sakamakon rashin amincewa da fenaritin da aka bai wa Morocco a ƙarshen wasan, yayin da ake kunnen doki babu ci.

Bayan an dakatar da wasan na tsawon mintuna 17, 'yan wasan Senegal sun dawo filin, amma ɗan wasan Morocco Brahim Diaz ya kasa cin fenaritin.

A ranar 25 ga Maris, Senegal ta shigar da ƙara a gaban Kotun CAS tana neman a soke hukuncin CAF tare da mayar mata da kofin da ta ce ta lashe a filin wasa.

Yanzu dai ana sa ran sauraren ƙarar zai gudana ne a ranar 8 ga Oktoba, inda za a yanke hukunci kan wannan takaddama mai ɗaukar hankali a fagen ƙwallon ƙafar Afirka.