Shahararren ɗan wasan bayan ƙasar Argentina, Nicolás Otamendi, ya sanar da yin ritaya daga bugawa ƙasarsa wasa yana da shekara 38.
Gasar Kofin Duniya ta 2026 ita ce ta huɗu da Otamendi ya halarta. Ya shiga wasan ƙarshe ne a matsayin wanda aka sauya, inda Argentina ta sha kashi da ci 1-0 a hannun Spain a ranar Lahadi.
A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Otamendi ya bayyana cewa sanarwar ritayar na daga cikin abubuwan da suka fi yi masa wuya a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.
"Yau na tsinci kaina ina rubuta kalmomi mafiya wuya a rayuwata ta ƙwallon ƙafa. Ina yin bankwana da tawagar ƙasata Argentina, amma zuciyata cike take da alfahari da farin cikin wakiltar ƙasata."
Otamendi ya shafe shekaru masu yawa yana kare launin Argentina, inda ya taka muhimmiyar rawa a nasarorin da ƙasar ta samu a manyan gasa na duniya.