Sufeto Janar na Ƴan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya umarci dukkan jami’an ‘yan sanda a faɗin ƙasar nan da su ɗauki mataki mai tsauri kan duk wanda aka samu yana riƙe da makamai ba bisa ƙa’ida ba, domin daƙile ayyukan ta’addanci da sauran laifukan da ke barazana ga tsaron al’umma.
Ya ce jami’an su yi aiki da tanadin Force Order 327 wajen gudanar da ayyukansu, musamman domin murƙushe masu aikata laifuka da kuma tabbatar da zaman lafiya, musamman a Jihar Benue da ke fama da hare-hare.
Sufeto Janar ɗin ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia, a birnin Makurdi, lokacin da ya kai ziyarar aiki jihar domin tantance halin tsaro bayan yawaitar kashe-kashe da hare-haren da ake fuskanta.
A yayin taron, mahalarta sun nuna matuƙar damuwa kan yadda hare-haren ke ci gaba da faruwa, tare da tambayar dalilin da ya sa wasu matsalolin tsaro ba sa kaucewa duk da bayanan sirri da ake bai wa hukumomin tsaro.
Haka kuma, Sufeto Janar ya buƙaci matasan Jihar Benue da su ƙara haɗa kai da jami’an tsaro ta hanyar samar da sahihan bayanan sirri, yana mai cewa hakan zai taimaka matuƙa wajen yaƙi da aikata laifuka.
A nasa ɓangaren, Gwamna Hyacinth Alia ya sake jaddada kira ga gwamnatin tarayya da ta amince da kafa ‘yan sandan jihohi, yana mai bayyana cewa hakan zai taimaka wajen inganta tsaro da kuma magance matsalolin da ke addabar jihohi daban-daban.