Wata Babbar Kotu a lardin Western Cape na Afirka ta Kudu ta dakatar da shirin Majalisar Dokokin ƙasar na tsige Shugaba Cyril Ramaphosa, kan zarge-zargen rashin ɗa'a da ake yi masa.

A hukuncin wucin gadi da kotun ta yanke ranar Juma'a, ta umarci majalisar da ta dakatar da duk wani mataki na tsige shugaban har sai an kammala sauraron ƙarar da Ramaphosa ya shigar yana ƙalubalantar rahoton kwamitin bincike.

Rahoton kwamitin ya bayyana cewa akwai hujjojin da ke nuna shugaban na da tambayoyin da zai amsa dangane da satar kuɗaɗe da aka yi daga gonarsa ta Phala Phala a shekarar 2020.

Lamarin ya shafi satar dala 580,000 na Amurka, kuɗin da Ramaphosa ya ce an samu ne daga sayar da shanun dawa. Sai dai masu sukar sa sun yi tambaya kan dalilin da ya sa aka ajiye irin waɗannan maƙudan kuɗaɗe a cikin wani kujera a gidansa.

Batun ya haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin Afirka ta Kudu tun bayan bayyana zargin.

A baya, Kotun Tsarin Mulkin ƙasar ta yanke hukuncin cewa Majalisar Dokoki ba ta bi ƙa'ida ba lokacin da ta yi watsi da rahoton kwamitin bincike, inda ta umarce ta da ta sake fara tsarin nazarin batun tsige shugaban.

Bayan wannan hukunci ne aka fara shirye-shiryen kafa kwamitin da zai jagoranci aikin tsige shugaban, amma Ramaphosa ya garzaya kotu domin neman a dakatar da shirin har sai an yanke hukunci kan ƙarar da ya shigar.

Shugaban ya ci gaba da musanta aikata wani laifi, yana mai cewa kuɗin da aka sace daga gonarsa kuɗaɗe ne na halal da aka samu daga kasuwanci.

Duk da rikicin siyasar, Ramaphosa na ci gaba da samun goyon bayan jam'iyyarsa ta African National Congress (ANC), wadda ke jagorantar gwamnatin haɗaka ta ƙasar. Ana sa ran rinjayen kujerun da ANC ke da su a majalisa zai iya hana duk wani yunƙurin tsige shugaban idan har aka ci gaba da shirin nan gaba.

An fara wannan rikici ne bayan tsohon shugaban hukumar leƙen asirin Afirka ta Kudu, Arthur Fraser, ya shigar da ƙara ga 'yan sanda yana zargin Ramaphosa da ɓoye satar miliyoyin daloli daga gonarsa ta Phala Phala.