Kwamandan Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA a Arewa maso Yamma, Manjo Janar W.B. Idris, ya bayyana cewa hare-haren sojoji da ake ci gaba da kai wa sun tilasta wa 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane barin manyan hanyoyi tare da tserewa zuwa cikin dazuka da ƙauyuka masu nisa.

Janar Idris ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da wakilan kafafen yaɗa labarai na fannin tsaro a Hedikwatar Operation FANSAN YAMMA da ke Gusau, Jihar Zamfara.

Ya ce hare-haren da sojoji suka kai na tsawon watanni, tare da amfani da sahihan bayanan sirri da sintiri a yankunan da ake fama da matsalar tsaro, sun raunana ƙarfin 'yan ta'addan tare da tilasta musu sauya dabarun kai hare-hare.

A cewarsa, a halin yanzu dakarun Operation FANSAN YAMMA na da cikakken iko kan mafi yawan manyan hanyoyin sufuri a yankin, lamarin da ya hana 'yan ta'adda gudanar da hare-hare a kan tituna kamar yadda suka saba a baya.

Ya bayyana cewa tsakanin watan Janairu da Afrilun 2026, rundunar ta samu gagarumar nasara a kusan kowane mako, inda ake ƙwato makamai da kuma kashe 'yan ta'adda da dama.

"A wannan lokaci, muna ƙwato matsakaicin bindigogi biyar a kowane mako, tare da kashe aƙalla 'yan ta'adda goma. Wannan matsin lamba ya tilasta musu sauya dabarunsu da kuma guje wa arangama kai tsaye da sojoji," in ji shi.

Kwamandan ya ce yanzu masu aikata laifukan sun koma ɓuya a cikin dazuka, yankunan duwatsu da ƙauyuka masu nisa, inda suke kai hare-hare kan manoma da al'ummomin karkara masu rauni.

Ya ƙara da cewa wannan ne ke sa wasu ke tunanin babu jami'an tsaro a yankunan, alhali hare-haren na faruwa ne a wurare masu matuƙar wahalar isa.

Janar Idris ya kuma bayyana cewa damina ta ƙara kawo cikas ga ayyukan sojoji, saboda hanyoyi suna lalacewa tare da hana manyan motocin yaƙi shiga yankunan da 'yan ta'adda ke buya.

Ya ce motocin yaƙi irin su masu ɗaukar tan biyar, bakwai da goma suna fuskantar matsalar zirga-zirga a hanyoyin karkara da suka yi laushi ko ambaliya ta mamaye su.

Sai dai ya jaddada cewa duk da waɗannan ƙalubale, rundunar za ta ci gaba da gudanar da hare-hare da suka dogara da bayanan sirri domin fatattakar 'yan ta'adda da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma a yankin Arewa maso Yamma.