Gwamnatin Jihar Sokoto ta ayyana Juma'a, 24 ga Yulin 2026, a matsayin ranar hutu ga ma'aikatan gwamnati domin ba su damar shiga aikin rajistar masu kaɗa ƙuri'a da kuma samun Katin Zaɓe na Dindindin (PVC).

Gwamnan jihar, Ahmed Aliyu, ya buƙaci dukkan ma'aikatan gwamnati da suka kai shekarun yin zaɓe amma ba su yi rajista ba, su yi amfani da wannan damar wajen yin rajista domin su sami damar cika haƙƙinsu na ɗan ƙasa a babban zaɓen da ke tafe.

A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a na Gwamna, Abubakar Bawa, ya fitar, an bayyana cewa gwamnatin jihar na ci gaba da tabbatar da cewa ma'aikatan gwamnati sun samu cikakkiyar dama ta shiga ayyukan ƙasa da kuma amfani da haƙƙoƙinsu na dimokuraɗiyya.

Sanarwar ta kuma yi kira ga sauran al'ummar jihar da ba su yi rajistar zaɓe ba ko kuma waɗanda suka kai shekarun yin rajista a baya-bayan nan, da su yi amfani da ƙarin makonni biyu da Hukumar Zaɓe ta bayar domin yin rajista da karɓar katin zaɓensu.

An bayyana cewa wa'adin ƙarin makonni biyun da aka bayar domin ci gaba da rajistar masu kaɗa ƙuri'a zai ƙare ne a ranar Lahadi, 26 ga Yulin 2026.