Ƙasashen mambobin Ƙungiyar Sadarwa ta Afirka (African Telecommunications Union – ATU) sun amince da Sanarwar Abuja ta 2026 kan Ingantacciyar Haɗin Intanet a Afirka (Abuja 2026 Declaration on Meaningful Connectivity), a wani mataki da ke nuna sabon babi a tafiyar sauyin fasahar dijital a nahiyar.

An cimma matsayar ne a yayin Taro na Bakwai na Wakilan Ƙasashen Mambobi (7th Ordinary Session of the Conference of Plenipotentiaries) da ke gudana a Abuja, inda aka tsara muhimman abubuwan da za su jagoranci ci gaban fasahar dijital a Afirka.

Sanarwar ta mayar da hankali kan muhimman fannoni da suka haɗa da tabbatar da kowa ya samu damar amfani da fasahar dijital, faɗaɗa amfani da intanet mai araha, bunƙasa da kare kayayyakin sadarwa, daidaita dokoki da ƙa'idoji tsakanin ƙasashe, haɓaka ƙwarewar ma'aikata, tabbatar da 'yancin Afirka a fannin fasahar dijital, kare haƙƙin masu amfani da fasahar sadarwa da kuma samar da manufofin haraji masu adalci.

Haka kuma, sanarwar ta buƙaci Hukumar Tarayyar Afirka (AU Commission), Ƙungiyar Sadarwa ta Duniya (ITU), ƙungiyoyin tattalin arzikin yankuna, abokan hulɗar ci gaba, kamfanonin fasaha, cibiyoyin ilimi da ƙungiyoyin farar hula su ƙarfafa haɗin gwiwa domin tabbatar da cewa dukkan 'yan Afirka sun amfana da ingantacciyar haɗin intanet, tare da taimakawa wajen cimma Manufofin Ci Gaba Mai Ɗorewa na Majalisar Ɗinkin Duniya (SDGs).

Ƙasashen mambobin ƙungiyar sun kuma yi kira da a gaggauta aiwatar da matakan da sanarwar ta ƙunsa cikin haɗin kai, yayin da aka buƙaci masu samar da ayyukan sadarwa da sauran abokan hulɗa a fannin fasaha su ƙara zuba jari cikin gaskiya da haɗin gwiwa domin rage gibin haɗin intanet a Afirka, tare da tabbatar da cewa al'ummomin nahiyar sun amfana da sauyin fasahar dijital ba tare da nuna bambanci ba.