Taron Kasa da Kasa na Bakwai na Babban Taron Wakilan Ƙungiyar Sadarwa ta Afirka (African Telecommunications Union – ATU) na gudana a Abuja, inda ƙasashen nahiyar ke tattauna hanyoyin gina ƙarfin fasahar zamani da makomar tattalin arzikin dijital na Afirka.
A yayin taron, ƙasashen Afirka sun bayyana aniyarsu ta taka muhimmiyar rawa wajen ƙirƙira da tsara fasahohi, manufofi da matakan da suka shafi basirar wucin gadi (Artificial Intelligence – AI), tsaron yanar gizo (Cybersecurity), sadarwa, haɗa kowa cikin duniyar dijital (Digital Inclusion) da sauran fannoni na fasahar sadarwa da za su tsara makomar nahiyar.
Mahalarta taron sun jaddada cewa lokaci ya yi da Afirka za ta daina kasancewa mai amfani da fasahohi da manufofin da wasu ƙasashe suka ƙirƙira kawai. Maimakon haka, sun ce ya zama dole nahiyar ta kasance cikin masu ƙirƙirar sabbin fasahohi, samar da sababbin kirkire-kirkire da kuma tsara manufofin da za su jagoranci ci gabanta.
Ƙasashen sun kuma amince da ƙarfafa haɗin gwiwa domin tabbatar da cewa ana haɓaka fasahohi da suka dace da buƙatu, al'adu da muradun al'ummar Afirka.
Daya daga cikin muhimman shirye-shiryen da aka tattauna shi ne samar da samfurin basirar wucin gadi na Afirka (African AI Language Model), wanda zai haɗa manyan harsunan Afirka domin tabbatar da cewa harsuna da al'adun nahiyar sun samu wakilci a sabbin fasahohin zamani.
Ƙasashen mambobin ƙungiyar sun bayyana cikakken goyon bayansu ga wannan shiri, tare da sake jaddada muhimmancin haɗin kai da magana da murya ɗaya domin ƙarfafa matsayin Afirka a fagen fasahar dijital na duniya.