Majalisar Dattawan Najeriya ta yi barazanar kakaba takunkumi kan wasu Ma'aikatun Gwamnati, Hukumomi da Kamfanonin Gwamnati (MDAs da GOEs) da ke ci gaba da yin watsi da gayyatar da take musu domin gudanar da aikin sa ido da kundin tsarin mulki ya ɗora mata.

A zaman majalisar na ranar Alhamis, Shugaban Kwamitin Kudi na Majalisar Dattawa ya sanar da cewa binciken da kwamitin ke gudanarwa kan yadda ma'aikatun da hukumomin gwamnati ke tafiyar da harkokin kuɗinsu na fuskantar cikas saboda rashin haɗin kai daga wasu hukumomi.

Majalisar ta jaddada cewa halartar gayyatar da take yi ba zaɓi ba ne, domin doka ta wajabta wa dukkan hukumomin gwamnati bin tanade-tanaden Dokar Alhakin Kasafin Kuɗi (Fiscal Responsibility Act).

A cewar majalisar, dole ne hukumomin su gabatar da bayanai kan kuɗaɗen shiga da suke samu da kansu (Internally Generated Revenue), kuɗaɗen harajin tambari (Stamp Duties), rarar kuɗaɗen gudanar da aiki (Operating Surplus), da kuma duk wasu kuɗaɗen da doka ta tanada a mayar da su cikin Asusun Haɗaɗɗen Kuɗaɗen Shiga na Tarayya (Consolidated Revenue Fund).

Majalisar Dattawa ta kuma buƙaci Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya da ministoci su tabbatar da cewa duk hukumomin da ke ƙarƙashinsu sun bi umarnin majalisar tare da cika dukkan ƙa'idojin da doka ta tanada.

Majalisar ta yi gargaɗin cewa za ta ɗauki matakan ladabtarwa kan duk wata hukuma ko ma'aikata da ta ci gaba da ƙin ba da haɗin kai ga ayyukan sa ido da take gudanarwa.