Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ya tanadi kafa Rundunar 'Yan Sandan Jihohi (State Police) a faɗin ƙasar.

An cimma wannan matsaya ne bayan nazari da kaɗa ƙuri'a kan kudirin da bangaren zartarwa ya gabatar, a zaman Kwamitin Dukkan Majalisar (Committee of the Whole) ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen.

Duk da ɗan cece-kuce da ya barke yayin zaman, Kakakin Majalisar ya sanar da cewa 'yan majalisa 311 ne suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da kudirin.

Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu, wanda ya jagoranci muhawarar kudirin, ya bayyana cewa manufar gyaran kundin tsarin mulkin ita ce ƙarfafa tsarin tarayya na Najeriya ta hanyar bai wa jihohi damar kafa rundunonin 'yan sanda na kansu.

Ya ce matakin zai taimaka wajen inganta tsaron rayuka da dukiyoyi, da kusantar ayyukan tsaro ga al'umma, tare da bai wa gwamnatocin jihohi ƙarin rawa wajen magance matsalolin tsaro a yankunansu.

Sai dai kudirin na buƙatar kammala sauran matakan da kundin tsarin mulki ya tanada kafin ya zama doka, ciki har da amincewar Majalisar Dattawa da kuma samun goyon bayan mafi yawan majalisun dokokin jihohi.