Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da ƙaƙaba sabbin harajin shigo da kayayyaki daga ƙasashe da dama, ciki har da Najeriya, a wani mataki na ƙarfafa manufofinsa na kare masana'antun cikin gida.
Sabbin harajin, waɗanda suka kai tsakanin kashi 10 zuwa 12.5 cikin 100, sun shafi kayayyakin da ake shigarwa Amurka daga wasu ƙasashe. Gwamnatin Trump ta ce matakin ya samo asali ne daga zargin cewa wasu abokan hulɗar kasuwancin Amurka ba sa ɗaukar isassun matakan da suka dace wajen yaƙi da ayyukan tilasta wa mutane yin aiki.
Sabon tsarin harajin ya maye gurbin wani haraji na wucin gadi da aka aiwatar bayan da Kotun Ƙolin Amurka ta soke wani jerin haraje da gwamnatin Trump ta kakaba a baya.
Sai dai matakin ya haifar da martani daga ƙasashe da dama. Brazil da Australia sun bayyana cewa ba su ga wani dalili da zai tabbatar da ƙaƙaba musu sabon harajin ba.
Haka kuma, Japan ta bayyana matakin a matsayin abin takaici, yayin da New Zealand ta ce ta yi matuƙar takaici da sabon tsarin harajin da gwamnatin Amurka ta sanar.
Masana tattalin arziki na ganin cewa irin waɗannan matakai na iya ƙara ta'azzara takaddamar kasuwanci tsakanin Amurka da wasu ƙasashe, tare da yin tasiri ga kasuwannin duniya idan aka ci gaba da aiwatar da su.