Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai Zaman Kanta (ICPC) ta bayyana cewa ta gano yadda Rundunar 'Yan Sandan Najeriya da wasu ma'aikatun gwamnati biyar suka fi sauran hukumomi yawan jami'an bogi a tsarin biyan albashin gwamnati.
Shugaban hukumar, Musa Adamu Aliyu, ne ya bayyana hakan yayin da yake sanar da sakamakon binciken da ICPC ta gudanar kan tsarin biyan albashin ma'aikatan gwamnati.
A cewarsa, binciken ya gano aƙalla jami'ai 908 da ake zargin na bogi ne a ma'aikatu da hukumomi 59 na gwamnati.
ICPC ta ce binciken ya kuma kai ga ƙwato kusan naira miliyan 942, kuɗaɗen da aka biya waɗannan jami'an bogi a matsayin albashi.
Hukumar ta ce binciken na daga cikin matakan da take ɗauka na tsaftace tsarin biyan albashi, hana almundahana da tabbatar da cewa kuɗaɗen gwamnati suna zuwa ga ma'aikatan da suka cancanta.