Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa wasu mutum uku hukuncin ɗaurin rai da rai bayan ta same su da laifin hannu a garkuwa da ɗalibai da malamansu a ƙaramar hukumar Oriire da ke jihar Oyo.
Alƙalin kotun, Mai Shari'a Salim Ibrahim, ya ce an yanke hukuncin ne bayan waɗanda ake tuhuma sun amsa dukkan laifukan da aka gabatar a kansu.
Waɗanda aka yanke wa hukuncin su ne Abdulrazak Umar, wanda aka fi sani da Abu Khalifa ko Abu Khalid, Yunusa Musa, wanda aka fi sani da Yunusa Bin Musa, da kuma Shamsu Adamu Sani, wanda aka fi sani da Abu Itisar. Dukkansu 'yan asalin jihar Neja ne.
Kotun ta same su da laifukan ɓoye bayanan mutane masu alaƙa da ta'addanci, garkuwa da mutane, da kuma amfani da dandalin saƙonni wajen shirya da horas da ayyukan ta'addanci.
Mai Shari'a Salim Ibrahim ya bayyana cewa mutanen ukun mambobi ne na ƙungiyar Darul Salam, wadda ke biyayya ga ƙungiyar Ansaru.
Hukuncin ya zo ne mako guda bayan Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci kan wasu manyan kwamandojin ƙungiyar Ansaru da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gurfanar a gaban kotu bisa laifukan da suka shafi ta'addanci.