Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta yi zargin cewa Amurka ta yi amfani da jiragen yaƙin B-1 da ke sansanin sojin sama na Fairford da ke Birtaniya wajen kai hare-hare kan Iran.

IRGC ta gargaɗi Birtaniya cewa duk wani sansani da aka yi amfani da shi wajen kai wa Iran hari za a ɗauke shi a matsayin halastaccen wurin kai hari idan rikicin ya ƙara tsananta.

Haka kuma, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah-wadai da abin da ta bayyana a matsayin bai wa Amurka damar amfani da sansanonin soja da kayayyakin Birtaniya wajen kai hare-haren. Ta ce duk wata ƙasa da ta bayar da irin wannan gudunmawa za a ɗauke ta a matsayin mai shiga yaƙin kai tsaye.

IRGC ta kuma yi zargin cewa Amurka ta koma amfani da jiragen yaƙin B-1 ne bayan raguwar makamai masu linzami masu shawagi da take da su a Tekun Indiya.

Sai dai, har zuwa yanzu babu wata hujja mai zaman kanta da ta tabbatar da waɗannan zarge-zargen.

A wani iƙirari kuma, IRGC ta ce ta kai hare-hare kan wata rundunar yaƙin lantarki ta Amurka da ke sansanin Al-Adiri, da cibiyar hutawar sojojin Amurka, da kuma hasumiyar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta sansanin. Ta ce harin ya yi sanadin mutuwa ko raunata wasu sojojin Amurka.

Sai dai har yanzu babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan iƙirari.