Farashin ɗanyen man fetur a kasuwar duniya ya kai dala 100 kowace ganga, karo na farko tun watan Mayu, sakamakon tsanantar rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ɗanyen mai samfurin Brent, wanda ake amfani da shi a matsayin ma'aunin farashin mai a duniya, ya ƙaru da sama da kashi shida cikin ɗari a ranar Alhamis. Hauhawar ta biyo bayan ci gaba da hare-haren da Amurka ke kai wa Iran da kuma ƙarin fargabar da rikicin ya haifar a kasuwannin makamashi.

Haka kuma, hare-haren da mayaƙan Houthi na Yemen suka kai kan jiragen dakon mai a Tekun Maliya sun ƙara tayar da hankalin masu zuba jari, domin sun shafi wata muhimmiyar hanyar jigilar mai da Saudiyya ke amfani da ita domin kauce wa mashigar Hormuz.

Ba farashin mai kaɗai ba ne ya tashi. Farashin iskar gas ma ya ci gaba da ƙaruwa a cikin watan da ya gabata, inda ma’aunin farashin gas na Birtaniya ya haura zuwa kusan fan 150 kan kowace tama, idan aka kwatanta da kusan fan 98 a ƙarshen watan Yuni.

Masana tattalin arziki na ganin cewa ci gaba da hauhawar farashin mai da iskar gas na iya haifar da ƙarin hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa a ƙasashe da dama na duniya, musamman idan rikicin Gabas ta Tsakiya ya ci gaba da ƙamari.