Gwamnatin Birtaniya ta sanar da janye sauran jami'anta daga ofishin jakadancinta da ke Tehran, sakamakon tabarbarewar yanayin tsaro da rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin Amurka da Iran.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Birtaniya ta ce an ɗauki matakin ne na wucin gadi domin kare lafiyar jami'anta, tana mai cewa ofishin jakadancin da ke Tehran zai ci gaba da gudanar da wasu ayyukansa daga nesa.

Wannan mataki ya biyo bayan sanarwar da Birtaniya ta yi kusan wata guda da ya gabata na janye wasu daga cikin jami'anta daga Iran. Haka kuma, ta bi sahun wasu ƙasashen Turai da Australia da New Zealand wajen dakatar da ayyukan ofisoshin jakadancinsu a Tehran.

A cikin wata sanarwa, Ma'aikatar Harkokin Wajen Birtaniya ta yi gargaɗi ga 'yan ƙasarta da ke Iran cewa suna fuskantar haɗarin kama su, yi musu tambayoyi ko tsare su na wani lokaci.

Sanarwar ta ce mallakar fasfo ɗin Birtaniya ko kuma zargin mutum yana da alaƙa da Birtaniya kaɗai na iya zama dalilin kama shi, inda ta yi gargaɗin cewa wasu na iya shafe watanni ko ma shekaru a tsare.

Birtaniya ta kuma shawarci 'yan ƙasarta da su guji tafiya zuwa Iran, tare da ƙarfafa wa waɗanda ke cikin ƙasar su sake tantance ko ya dace su ci gaba da zama, la'akari da haɗarin da ake ciki.

Bugu da ƙari, ta buƙaci 'yan Birtaniya da ke yankin Gabas ta Tsakiya su kasance cikin shiri kan yiwuwar soke tashin jirage, rufe sararin samaniya na ɗan lokaci da kuma sauran matsalolin sufuri da ka iya tasowa sakamakon rikicin.