Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bayyana aniyarta ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa wasu mutum uku da aka samu da laifin garkuwa da ɗalibai a jihar Oyo.
A ranar Alhamis ne kotun ta yanke wa mutanen uku, waɗanda 'yan asalin jihar Neja ne, hukuncin ɗaurin rai da rai bayan ta same su da hannu a aikata laifin sace ɗaliban.
Sai dai DSS, wadda ita ce ta gurfanar da waɗanda ake tuhuma, ta ce hukuncin ɗaurin rai da rai bai dace da girman laifin da suka aikata ba.
Hukumar ta bayyana cewa za ta nemi kotun ɗaukaka ƙara ta sake duba hukuncin, tana mai jaddada cewa masu garkuwar sun kashe malamai biyu na makarantar yayin da suke tsare da su, abin da ya ƙara tsananta girman laifin.
DSS ta ce za ta ci gaba da amfani da duk hanyoyin shari'a domin tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa da kuma ƙarfafa yaƙi da masu aikata laifukan garkuwa da mutane a ƙasar.