Kannywood ta shafe shekaru tana fama da ƙalubale daga ciki da wajen masana’antar, matsalolin da a wasu lokuta kan janyo tsaiko ga harkokinta.

Daga cikin manyan matsalolin da suka fi ɗaukar hankali akwai rikice-rikicen cikin gida, musamman tsakanin Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano da wasu jarumai da masu shirya fina-finai.

An kafa hukumar ne a zamanin tsohon gwamnan Ibrahim Shekarau domin sanya ido kan yadda ake gudanar da harkokin fina-finai da bidiyo a jihar Kano. Tun daga lokacin, dokokin addini da al’ada sun kasance cikin abubuwan da ake ganin suna takaita ci gaban masana’antar.

Yayin da ake ci gaba da muhawara kan dakatar da jaruma Amina Uba da Adam Garba, ana tambayar ko irin waɗannan matakai na taimakawa wajen gyara ɗabi’u da inganta masana’antar.

A lokacin da Abubakar Rabo ke jagorantar hukumar, an yi ta kiraye-kirayen a mayar da shugabancin hukumar ƙarƙashin kulawar mutanen cikin masana’antar.

Sai dai daga zamanin Isma'ila Na'Abba Afakallah zuwa shugabancin Abba El-Mustapha na yanzu, an dakatar da jarumai da mawaƙa da dama, yayin da aka gurfanar da wasu har aka tura su gidan yari.