Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa mutane uku hukuncin ɗaurin rai da rai bayan ta same su da laifin hannu a sace ɗalibai da malamai a Ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo.


Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Abdulrazak Umar, wanda aka fi sani da Abu Khalifa ko Abu Khalid, Yunusa Musa (Yunusa bin Musa) da Shamsu Adamu Sani (Abu Itisar).


Mai shari’a Salim Ibrahim ne ya yanke hukuncin, inda ya bayyana cewa hukuncin ɗaurin rai da rai zai fara aiki daga ranar da aka kama waɗanda aka samu da laifin.


An gurfanar da mutanen uku kan tuhume-tuhume guda 10 da suka haɗa da ta’addanci, garkuwa da mutane, ɓoye bayanai, tunzura jama’a da kuma haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kuma zarge su da kasancewa mambobin ƙungiyar Darul Salam, wadda ake zargin tana da alaƙa da ƙungiyar Ansaru da aka haramta a ƙasar.


A yayin shari’ar, waɗanda ake tuhuma sun amsa wasu daga cikin laifukan da suka shafi ɓoye bayanai game da harin makarantar da kuma kasancewarsu mambobin ƙungiyar Darul Salam. Haka kuma, Abdulrazak Umar ya amsa ƙarin zargin bayar da horo da umarni ga mambobin ƙungiyar ta hanyar wani rukunin WhatsApp mai suna “The Oneness of Allah is the Foundation of Peace.”


Bayan sauraron hujjojin ɓangarorin biyu, kotun ta yi watsi da roƙon sassauci da lauyoyin waɗanda aka yanke wa hukuncin suka gabatar, tare da yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai.


Lamarin ya samo asali ne daga harin da wasu ’yan bindiga suka kai makarantu uku a yankunan Esiele da Yawota na Ƙaramar Hukumar Oriire a ranar 15 ga Mayun 2026, inda suka sace mutane 46, ciki har da ɗalibai 39 da malamai bakwai.


A yayin harin, mataimakin shugaban makarantar L.A. Primary School, Joel Adesiyan, ya rasu yayin ƙoƙarin tserewa, yayin da wani malamin lissafi, Michael Oyedokun, ya mutu a hannun masu garkuwa da shi.


Sojojin Najeriya sun ceto mutum 44 daga cikin waɗanda aka sace a ranar 10 ga Yulin 2026 bayan wani samame na musamman da suka kai maboyar masu garkuwa da mutanen a Old Oyo National Park. Rundunar sojin ta kuma kama wasu mutane takwas da ake zargin suna da hannu a lamarin.


Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa ba a biya kuɗin fansa ba kuma gwamnati ba ta yi wata yarjejeniya da masu garkuwa da mutanen ba, duk da rahotannin cewa sun nemi a biya su naira biliyan ɗaya tare da sakin wani kwamandansu da ke tsare.