Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya bayyana cewa gwamnonin jihohin Kudu maso Gabas biyar sun cimma matsaya ta mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a wa'adi na biyu.
Uzodimma, wanda shi ne shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas, ya bayyana hakan ne yayin wani taro da Majalisar Dattawan Jihar Imo da sarakunan gargajiya a Owerri.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta nuna ƙwazo wajen aiwatar da ayyukan ci gaba a yankin ƙarƙashin manufar Renewed Hope, yana mai cewa al'ummar yankin na duba aikin gwamnati ne ba siyasa ba.
A cewarsa, gwamnonin yankin sun yanke shawarar yin aiki tare da Shugaba Tinubu domin tabbatar da cewa Kudu maso Gabas ta kasance cikin tsarin ci gaban Najeriya.
Uzodimma ya ce nan ba da jimawa ba gwamnonin yankin za su kai ziyarar haɗin gwiwa ga Shugaba Tinubu domin ƙarfafa haɗin kai da gwamnatin tarayya.
Ya lissafa wasu manyan ayyukan da gwamnatin Tinubu ta aiwatar a yankin da suka haɗa da kafa Hukumar Bunƙasa Kudu maso Gabas (SEDC), sake gina layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri ta yankin Kudu maso Gabas, hanyoyin haɗa Gadar Neja ta Biyu, da kuma dawo da zirga-zirgar jirgin ƙasa tsakanin Fatakwal da Aba.
Gwamnan ya kuma ce jihohin yankin sun amfana da ƙarin kuɗaɗen rabon tarayya, inganta tsaro da kuma shirin bashin karatu na ɗalibai.