Shugaban gasar La Liga ta Spain, Javier Tebas, ya yi kira ga Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, da ya sauka daga muƙaminsa.

Tebas ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar La Gazzetta dello Sport ta Italiya, inda ya zargi Infantino da ɗaukar wasu matakai da, a cewarsa, ke iya yin illa ga tafiyar hukumar FIFA.

Ya kuma soki wasu sauye-sauyen da aka yi a gudanar da wasanni, ciki har da yawaitar hutun shan ruwa, wani ƙarin hutu da aka yi a wasan ƙarshe bayan kammala mintuna 45 na farkon wasa, da kuma batun janye jan katin da aka bai wa ɗan wasan Amurka, Folarin Balogun.

Haka kuma, Tebas ya nuna rashin amincewarsa da shirin faɗaɗa gasar cin Kofin Duniya zuwa ƙasashe 64.

Da aka tambaye shi ko yana ganin lokaci ya yi da Gianni Infantino zai sauka daga muƙaminsa, Tebas ya ce, "A ra'ayina, eh. Ina ganin lokacinsa ya yi."