Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya yaba da amincewar Majalisar Dokokin ƙasar da wata doka da za ta hana yara masu ƙasa da shekara 15 amfani da kafafen sada zumunta.
A cikin wani saƙo da ya wallafa tare da wasu bidiyo da ke nuna wasu matsalolin da matasa ke fuskanta, ciki har da matsalolin lafiyar kwakwalwa da na cin abinci, Macron ya ce Faransa ta ɗauki matakin ne domin kare yara daga illolin da ke tattare da amfani da kafafen sada zumunta.
Ya ƙara da cewa ƙasar na ƙoƙarin jagorantar sauran ƙasashen Turai wajen samar da ingantattun matakan kare matasa a duniyar intanet.
A ƙarƙashin dokar, kamfanonin da ke mallakar kafafen sada zumunta za su kasance wajibi su samar da hanyoyin tantance shekarun masu amfani da dandalolinsu.
Haka kuma, dokar ta tanadi hana amfani da wayoyin hannu a makarantun sakandare.
Idan dokar ta fara aiki kamar yadda aka tsara, daga watan Satumba duk wanda zai buɗe sabon shafi a kafar sada zumunta sai an tabbatar da shekarunsa, kuma duk wanda bai kai shekara 15 ba ba za a ba shi damar buɗe asusu ba.